Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na nahiyar Afrika – CAF Patrice Motsepe ya sanar da ƙasashen da za su ɗauki baƙuncin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na Afrika wato AFCON a 2025 da kuma wa da za a yi a 2027.
An sanar cewa ƙasar Moroko ce za ta karɓi baƙuncin gasar a 2025.
Kuma Wannan ne karo na biyu da za a buga gasar a ƙasar, wadda ta taɓa karɓar baƙuncin gasar a 1988.
Sannan kuma idan ba a manta ba, ita kanta kasar Moroko na cikin masu takarar ɗaukar baƙuncin gasar cin kofin duniya a 2030.
Ƙasashen Zambia Benin, Aljeriya da Najeriya ne suka janye wa Moroko domin ta karɓi bakuncin gasar a 2025.
Bayan haka hukumar CAF ta sanar cewa kasashen Kenya, Tanzania da Uganda za su ɗauki baƙuncin gasar a shekarar 2027 in Allah ya kai mu.
Rabon da a buga gasar a gabashin Afrika tun a shekarar 1976 lokacin da Habasha ta dauki bakunci. Sai dai kuma kasar Sudanta ma ta taba daukar baƙuncin gasar.
A ranar 13 ga watan Janairun 2024 ne za a fara buga gasar cin kofin AFCON ta 2024 a ƙasar Ivory Coast.
Najeriya na daga cikin waɗanda za su fafata a wannan gasa.
Discussion about this post