Sarkin Kano na 14, kuma Khalifar darikar Tijjaniya na dyuniya, Khalifa Sanusi Lamido Sanusi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su daina dora wa shugaban Kasa Bola Tinubu, laifin fadawa cikin tsananin matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar nan yanzu.
Sarki Sanusi ya fadi haka a lokacin da yake gabatar da Lakca a taron addini, da a wajen ne ya dan yi gajeruwar bayani game da halin da kasa Najeriya take ciki.
” Ba zan yi wa Tinubu a dalci ba idan na soki gwamnatin sa kan matsalolin da ake fama da su a kasar nan. Duk wanda ya karanci harkar tattalin arziki, tsimi da tanadi da harkar shige da ficen kudi a shekaru 8 ta suka gabata yasan cewa tabbas Najeriya za ta afka cikin wannan matsala. Ba laifin Tinubu bane ko kadan.
” Hasali ma Tinubun ne ke kokarin fiddo ‘yan Najeriya daga halin matsi da suke ciki. Musamman ta hanyar dakatar da biyan kudin tallafin mai ta ya yi bayan darewar sa kujerar gwamnati a 2023.
” Wannan matsala da ake mafa da shi a kasar nan, ba shine na farko ba, kasashe kamar su Venezuwela, Jamus, Uganda, Zimbabwe, duk sun yi fama da wannan matsala.
” Na fadi haka a Kaduna a gaban shugaba Tinubu cewa duk dan siyasar da ya ce muku wai za a samu sauki idan ya zama shugaban kasa, kada ku yarda dashi. Na fadi haka a wancan lokaci.
” Idan zan yi adalci kuma in yi wa Shugaba Bola Tinubu adalci, ba shi ne ya jawo wahalhalun da ake ciki a yanzu ba; tsawon shekaru takwas muna rayuwar karya ne kawai a kasar nan tare da bashi mai yawa daga basussukan kasashen waje da na cikin gida. Babban Bankin Najeriya na bin bashin sama da Naira Tiriliyan 30, wanda hakan ya sa bashin ya haura kashi 100 cikin 100.
” Tsakani da Allah, maganar tabarbarewar arziki da matsin da ake fama da shi a kasar nan, a yi wa Tinubu a dalci, babu ruwan sa, babu hannunsa a ciki. Kuma gaskiyar magana kenan. Idan ya kwafsa nan gaba zan fito in gaya masa gaskiya, Amma yanzu ba shi da laifin komai.
” (A cikin shekaru takwas da suka wuce, babban bankin Najeriya ya ci gaba da buga wasu kudade, kuma darajar Naira na ci gaba da faduwa. CBN na ta buga kudi babu gaira babu dalili, sannan darajar naira na ci gaba da faduwa.
Sannan gwamnati a wancan lokaci, ba su jin shawara, sai kaga dan mitsitsin yaro da bai san komai ba yana da gidaje a Dubai, da jirgin sama na sa, saboda an bude masa harkar siyar da dala, a bashi a naira 400, shi kuma ya saida naira 600 duk dala daya.
Roko na shine a ci gaba da hakuri, masu hali kuma su taimakawa marasa hali.
Discussion about this post