Yayin da Najeriya ta ɗauki tsatstsauran matakin rashin amincewa da juyin mulki a ECOWAS baki ɗaya, shi kuwa dattijo mawaƙin rawar kwatagwalci, Charly Boy, addu’a ya yi da fatan afkuwar juyin mulki a Najeriya.
Ya yi addu’ar a shafin sa na X, wanda a baya aka fi sani da Tiwita, cewa ya na fatan a yi juyin mulki.
Duk da dai Charly Boy bai fito ƙarara ya ambaci kalmar juyin mulki a rubutun na sa ba, amma dai ya yi addu’ar abin da ya faru a Burkina Faso, Mali, Najeriya da Gabon, ya faru a Najeriya ita ɗin ma.
Addu’ar Charly Boy:
“Ya Ubangiji, ya mu da ke nan Najeriya za mu riƙa yin addu’a, sai ka riƙa amsa addu’ar a Gabon, Nijar, Burkina Faso da Mali.”
Dukkan waɗannan ƙasashen huɗu dai sun koma hannun sojojin juyin mulki a yanzu haka.
Charly Boy dai bai bayyana dalilin sa ba, to amma dai a lokacin zaɓen shugaban ƙasa a 2023 ɗin nan, ya goyi bayan ɗan takarar jam’iyyar LP ne, Peter Obi.
Maganganun Charly Boy sun zo daidai lokacin da Najeriya ke a sahun gaba wajen ƙaƙaba wa Nijar takunkumi, tare da barazanar kai mata hari domin a kori sojoji daga mulkin ƙasar.
Wata ɗaya bayan juyin mulkin Nijar, sai Sojojin Gabon su ka hamɓarar da shugaba Ali Bongo a ranar Laraba.
Discussion about this post