Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 52, sun kama wasu 60 sannan sun ceto mutum 61 da aka yi garkuwa da su faɗin a kasar nan.
Dakarun sun samu wannan nasara tsakanin ranar 15 zuwa 22 ga Satumba.
Darektan yaɗa labarai na hukumar tsaron Edward Buba ya sanar da haka a ƙarshen makon jiya a Abuja.
Buba ya ce ƴan ta’adda mutum 7 da suka hada da maza biyar da mata biyu sun mika wuya.
Ya ce dakarun sun kama wadannan mahara da manyan bindigogi kiran AK-47 53, bindiga kirar Beretta daya, bindiga kirar hannu 18 da bindiga Pump action uku.
“Sauran makaman da aka kama sun hada da harsasai 650, AK-47 50 da harsasai masu yawa.
“Dakarun sun kama motoci 15, babura 12, Keke 12, wayoyin 5, adda 12, janareto biyu, tukunyar isakar gas, dabbobi 133, katin waya Airtel ta naira 8,000 da kudi naira N602,000.
Buba ya kara da cewa rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun kama bakin mai na sata da kudinsa ya kai naira miliyan 946.38 a Kudu maso Kudancin Najeriya.
Daga nan Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun ci gaba da kai wa mahara hari a Arewa maso Gabashin kasar nan.
Ya kuma ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji, Safe Haven, Whirl Punch da Whirl Stroke’ sun ci gaba da kai wa mahara hari a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Daga nan rundunar ‘Operation UDO KA da Operation Search and Flush’ dake Kudu maso Gabas sun ci gaba samun nasara a samar da tsaro a yankin.
“Dakarun sun kama ‘yan kungiyar IPOB/ESN mutum biyar a kananan hukumomin Ikwo da Ihiala dake jihohin Ebonyi da Anambra.
Discussion about this post