Ƴan sandan jihar Delta ta kama wata mata da ta kashe mijinta yayin da suke dambe.
Kakakin rundunar Bright Edafe wanda ya sanar da haka ranar Laraba a garin Warri ya ce wannan abin tashin hankali ya faru a kauyen Mosogat dake karamar hukumar Ethiope.
Edafe ya ce mijin Jakpor Efemini mai shekara 32 ya gamu da ajalinsa da misalin karfe 1:20 na ranar Talata a lokacin da matarsa ta kamo ‘ya’yan maraiman sa ta matse.
“Kafin wani abu Efemini ya fadi ya suma.
Ta ce an yi gaggawar kai mijin asibiti inda likita ya tabbatar cewa ya mutu.
Edafe ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike kuma idan aka gama bincike za a garzaya da ita kotu domin yanke mata hukunci.
Discussion about this post