Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa sun ƙaryata zargin cewa an yi masu watandar Naira miliyan 100 ga kowanen su, a matsayin kuɗin tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa, bayan cire tallafin fetur.
Kakakin Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce rahoton da ake yaɗawa wai an yi masu kasafin Naira miliyan 100 ga kowanen su, ƙarya ce tantagaryar ta.
Lamarin ya samo asali ne daga wani rahoto da aka watsa a ranar Alhamis cewa Mataimakin Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC, Christopher Onyeka, ya ce an raba wa kowane sanata Naira miliyan 100, a matsayin kuɗaɗen tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa bayan cire tallafin fetur, “alhali an raba wa ‘yan Najeriya marasa galihu shinkafa da masara.”
Sanatocin Najeriya su 109, ta a bakin kakakin su, sun haƙiƙice cewa zargin wata mummunar manufa ce domin a ingiza talakawa a kan su.
“Shin waɗannan masu mugun nufin me su ke son cimmawa ne daga wannan sharri da ƙarya da suka kantara wa ‘Yan Majalisa?
“Babu wanda ya bai wa Sanatoci Naira miliyan 100 ko wani abu makamancin haka.
“Shin daga wane kasafin aka kafci kuɗaɗen aka raba mana? Wannan zargi sheɗanci daga wasu kafafen yaɗa labarai da kurbatsatstsun ‘yan siyasa domin su tozarta Sanatocin Najeriya.
Haka ita ma Majalisar Tarayya ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran su, Akin Rotimi, sun ƙaryata zargin su ma an raba wa kowanen su naira miliyan 100 a matsayin kuɗaɗen tallafi.
Adaramodu cewa ya yi Majalisar Tarayya ba za ta ɓata lokaci ba wajen gaggauta maka duk wani mai yaɗa wannan ƙarairayi a kan su.
Discussion about this post