‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun fille kan wani DPOn ƴan sanda mai suna Bako Angbashim dake aiki a Ahoada, karamar hukumar Ahoda jihar Ribas.
Maharan sun fille kan jami’in tsaron ranar Juma’a amma kuma rundunar ƴan sanda na zargin ‘yan kungiyar asiri masu suna ‘Iceland’ dake kauyen Odemude ne suka kashe jami’in tsaron.
Majiya daga rundunar ‘yan sanda ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun dana wa DPO din daka tafiya tare da wasu jami’an tsaro tarko ne yayin da suke hanyarsu na kai far wa maɓoyar maharan dake yankin.
A wani bidiyon da ya kareda kafafen sada zumunta a yanar gizo an nuna kai, hannu da wasu sassan jikin DPOn da maharan suka yi gunduwa-gunduwa da shi.
A bidiyon an ga yadda maharan ke rawa suna raira wakokokin cin nasara yayin da gawan jami’in tsaron na kwance a kasa.
Kakakin rundunar Grace Iringe-Koko ta tabbatar da kisan DPO din a wata takarda da ta fitar ranar Asabar.
Bisa ga takardan Grace ta ce marigayi Angbashim ya gamu da ajalinsa ranar Juma’a yayin da ya je kai dauki wa ‘yan sandan dake bata kashi da ‘yan kungiyar asiri.
“Duk jami’an tsaron da su ka yi arangama da ‘yan kungiyar asirin sun dawo da ransu shi Angbashim ya mutu.
Kwamishinan ‘yan sanda Polycarp Nwonyi ya bada umarnin gudanar da bincike domin kamo maharan.
Discussion about this post