Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah na Jihar Kwara, Bello Abubakar, ya yi roƙon cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa Fulani makiyaya kayan tallafi, domin su ma su rage raɗaɗin tsadar rayuwa.
Bello Abubakar ya yi wannan kira a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Ilorin, a ranar Litinin.
Ya ce Fulani sun fi kowa fama da raɗaɗin tsadar rayuwa a halin da ake ciki.
Ya ce akasarin makiyaya ba su da asusun ajiyar kuɗaɗe a bankuna, inda za su riƙa karɓar kuɗaɗe idan buƙatar hakan ya tashi.
Ya ce makiyaya na kashe kuɗi sosai wajen biyan mota a kai masu shanu kasuwa, domin su sayar.
Shugaban na Miyetti Allah ya nuna damuwa dangane da tsadar abinci a kasuwanni.
Daga nan sai ya bai wa Gwamnatin Tarayya shawara cewa baya ga raba tallafin abinci da gwamnatin ke yi, to kuma ya kamata ta fito da kayan abinci daga rumbunan ta, domin ta riƙa sayar wa talakawa a kan farashi mai rahusa.
Daga nan ya ƙara yin kira gwamnati ta taimaka wa makiyaya da allurai domin magance wasu cututtukan da ke kashe masu shanu.
Sannan ya ce sun gargaɗi Fulani matasa su nisanci aikata laifuka. Kuma sun yi kira a samu zaman sulhu tsakanin makiyaya da manoma, domin wanzar da zaman lafiya a yankunan karkara.
Discussion about this post