Ganin yadda Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta mamaye Majalisar Ƙasa a ranar Laraba, Majalisar Dattawa ta yi masu alƙawarin biya masu buƙatun su a cikin kwanaki bakwai masu zuwa.
Ƙungiyar ta Ma’aikatan Ƙwadago ta Najeriya ta mamaye harabar Majalisa a ranar Laraba, domin nuna fushi da damuwar su kan ƙarin tsadar rayuwa da aka afka a faɗin ƙasar nan, tun bayan hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya ƙara zafafa halin ƙunci da tsananin raɗaɗin tsadar rayuwa, tun a ranar da aka rantsar da shi, inda ya yi wa ‘yan Najeriya mummunan albishir na janye tallafin fetur nan take.
Masu zanga-zanga a Abuja sun darkaki Majalisar Dattawa a bisa jagorancin Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero da Festus Osifo, Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa, TUC.
A cikin fushi su ka darkaki Majalisar Ƙasa daga wurin da suka fara yin mahaɗa da cincirindo, kusa da otal ɗin Trsnscorp.
Mamayar da su ka yi wa Majalisa ta tilasta an tsayar da tantance mai ministocin da Bola Tinubu ya aika da sunayen su, da ake ci gaba da tantancewa tun daga ranar Litinin.
Masu zanga-zanga sun ce ba su iya ciyar ciyar da iyalan su, har kuma a lokaci guda su iya fita zuwa wuraren aikin su.
Sun jaddada cewa malejin tsadar rayuwa ya cilla sama sosai, har lamarin ya yi matuƙar muni.
Sanatan Barno ta Tsakiya, Ali Ndume ne aka tura masu ya je ya ba su haƙuri, kuma ya roƙi masu zanga-zangar su bai wa Majalisar Dattawa kwanaki bakwai domin a biya dukkan buƙatu da ƙorafe-ƙorafen da su ka gabatar.
Ita ma Sanatar FCT Abuja, Ireti Kingibe, ta roƙi masu zanga-zangar su bada kwanaki bakwai domin su tabbatar an magance matsalolin da su ka haddasa zanga-zangar.
Ta ce a “wannan karon Majalisar Dattawa ba za ta watsa masu ƙasa a ido ba.”
Discussion about this post