Ministan Tsaro Mohammed Badaru, ya ce Najeriya za ta dangantaka da Birtaniya, domin samun nasarar daƙile matsalar tsaro.
Badaru ya yi wannan bayani lokacin da ya ke karɓar baƙuncin Ministan Sojoji da Tsoffin Sojojin Birtaniya, James Heappey, a ofishin sa.
Bayanin na cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta Ma’aikatar Tsaro, Victoria Agba-Attah ta fitar.
Baduru ya ce Birtaniya na bayar ga gagarimar gudummawar tabbatar da tsaro a ruwan Najeriya.
Ya matsalar tsaro sha-kundum ce wadda ke tattare da ƙalubale masu tarin yawa.
Ya ce Sojojin Najeriya da na Birtaniya za su ci gaba da yin aiki tare domin ratattakar Boko Haram.
Ya ƙara da cewa Najeriya na matuƙar buƙatar taimakon Turai ta Yamma kamar yadda Turai ta Yamma ke taimakon sauran ƙasashe.
A na sa jawabin, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ce Gwamnatin Tarayya ta hau harya ɗoɗar domin danganawa maƙurar daƙile Boko Haram.
Kafin nan kuwa, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Tsaro, Ibrahim Kana, ya ce Birtaniya ce ƙololuwa a jerin ƙasashen da ke ƙawance da Najeriya.
Discussion about this post