Shugaban Mulkin Sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya bayyana cewa za su sauka su bayar da mulki ga farar hula nan da shekaru uku.
Tchiani ya yi wannan bayani kai-tsaye a ranar Asabar a gidan talabijin, bayan ganawar sa da tawagar sasantawar da ECOWAS ta sake tura masa, a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa, Abdulsalami Abubakar, da Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar III.
Kafofin yaɗa labarai na ciki har da BBC da Daily Trust, sun ruwaito cewa Tchiani ya ce nan da wata ɗaya za a kafa kwamitin sake rubuta kundin tsarin mulkin Nijar.
Da ya ke magana ta gidan talbijin da daren ranar Asabar, a lokacin tawagar ECOWAS na cikin ƙasar, ba a san dai irin yadda shugabannin ECOWAS za su maida masa raddin amincewa ko rashin amincewa da jawabin na sa ba.
Ya ce Nijar ba ta so ta yi yaƙi, sannan kuma ƙofa a buɗe ta ke domin ci gaba da tattaunawa da. Sai dai kuma ya ƙara da cewa za su kare kan su da ƙasar su idan hakan ya zama tilas.
Haka kuma a ranar Asabar ɗin ranar da ya gana da tawagar ECOWAS, Tchiani ya gana da wata tawagar daga Majalisar Ɗinkin Duniya (UN).
A ranar Asabar ɗin dai daga Yamai, Abdulsalami Abubakar ya ce sun gana da shugabannin mulkin soja na Nijar, kuma an buɗe ƙofar ci gaba da tattaunawa.
Tawagar ECOWAS ɗin dai ta samu tarba a filin jirgin saman Yamai daga Firayi Ministan Nijar, Ali Lamine Zeine.
Tawagar ta gana da Janar Abdourahmane Tchiani tsawon mintina 90, daga bisani kuma ta gana da hamɓararren Shugaban Ƙasa, Mohammed Bazoum.
Sai dai kuma Abdulsalami bai bayyana wa manema labarai irin abin da suka tattauna da Bazoum ba.
“Mun gana da Bazoum, kuma mun ji na sa bayanin dangane da abin da ya faru. Ya shaida mana abin da aka yi masa, da kuma ƙalubalen da yake fuskanta. Za mu sanar wa shugabannin ECOWAS abin da ya shaida mana.
“Duk da haka ƙofofin ci gaba da tattauna neman maslaha a buɗe su ke, domin a samu yadda za a sulhunta taƙaddamar a cikin lalama.” Inji Abdulsalami Abubakar.
A makon da ya gabata CNN ta ruwaito cewa Bazoum ya yi wa wani abokin sa saƙon ‘tes’ cewa an hana shi ganin kowa, kuma babu wutar lantarki a inda ya ke tsare.
Kuma ya yi ƙorafin abincin da ake kai masa kan lalace saboda babu wutar lantarkin adana kayan abinci.
Nijar dai babu wutar lantarki tun bayan da Najeriya ta katse wutar. Akasari an dogara ne da janareto da kuma sola.
Bazoum ya yi ƙorafin cewa saboda lalacewar kayan abinci, sai ya koma ya na cin gurasa da shinkafa kawai.
Sai dai kuma Janar Tchiani ya shaida wa tawagar Malaman Musulunci da su ka je Nijar daga Najeriya cewa ana ba Bazoum duk abincin da ya ke so, ba a ƙwace wayar sa ba, an haɗa shi da likitan sa, kuma ba a wulaƙantaccen wuri ya ke tsare ba.
Shirye-shiryen Gwabza Yaƙi: Mali Da Burkina Faso Sun Girke Jiragen Yaƙi A Nijar:
A ranar Asabar ce ƙasashen Burkina Faso da Mali suka fara girke jiragen yaƙi a Nijar, bayan Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS sun ce umarni kawai su ke jira, su afka wa Nijar da yaƙi.
Dama tun da farko sai da Mali, Burkina Faso da Gini su ka ce duk wanda ya ɗaura yaƙi da Nijar, to za su taya Nijar kare kan ta.
A cikin wata sanarwar haɗin-guiwa da suka fitar, sun ce “sakamakon afka wa Nijar da yaƙi, lamarin ba zai yi daɗi ba, zai haifar da mummunan bala’i a Afrika ta Yamma.”
Gidan Talbijin na Nijar ne ya sanar da fara girke jiragen jaƙin da Mali da Burkina Faso suka yi a ƙasar.
“Shugabannin Sojojin Mali da Burkina Faso sun yi taron gaggawa tare da na Nijar, a ranar Juma’a a Yamai. Sun gana ne domin ɗaukar matakan da suka dace, idan har ECOWAS ta zaɓi a yi yaƙi.”
Ƙasashen Cape Verde, Mali, Burkina Faso da Gini ba su goyon bayan ECOWAS ta kai yaƙi cikin Nijar.
Rikicin Nijar: ‘Ba Abin Da Zai Samu Bazoum’ – Firayi Ministan Nijar
Firayi Ministan Nijar wanda Sojojin Mulki Suka Naɗa, Ali Mahaman Lamine, ya bayar da tabbacin cewa ba abin da zai samu Bazoum.
Shugaban ECOWAS Bola Tinubu na Nijeriya ne dai a ranar Juma’a ya ce, Nijar za ta yaba wa aya zaƙi matsawar rashin lafiyar Bazoum ya tsananta.
“Babu abin da zai samu Bazoum, saboda mu a Nijar ba mu da al’adar tayar da hargitsi.” Haka ya shaida wa Jaridar New York Times.
Rikicin Nijar: Dubban Matasa Na Amsa Kiran Shiga Aikin Sojan-sa-kai’
Gidan Radiyon Radio France International ya ruwaito cewa dubban jama’a, akasari matasa na amsa kira tare da yin balantiyar fitowa amsa kiran shiga aikin sojan-sa-kai, domin shiga yaƙin taimaka wa sojojin Nijar.
Gidan radiyon ya ce a ranar Asabar dafifin mutane sun kai kan su a tsakiyar Yamai domin yin rajistar shiga aikin sa-kai.
Discussion about this post