Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara yi wa mata masu shekaru 9 zuwa 15 allurar rigakafin cutar dajin dake kama mahaifa daga ranar 25 ga Satumba.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na kasa NPHCDA Faisal Shuaib ya sanar da haka a taron da aka yi da sarakuna da malaman addini kan inganta cibiyoyin kiwon lafiya ranar Litini a Abuja.
Cutar dajin dake kama mahaifa
Cutar dajin dake kama mahaifa na daga cikin nau’ukan cutar daji na hudu dake kashe mutane a duniya.
Jami’an lafiya sun ce cutar ta yi ajalin mata 311,000 a duniya a shekarar 2018.
Sakamakon binciken Lancent ya nuna cewa mata miliyan 44 na cikin hadarin kamuwa da cutar daga shekarar 2020 zuwa 2069.
Binciken ya Kuma nuna cewa za a samu karin kashi 50% a yawan matan da cutar ke kashewa a duniya a 2040.
Zuwa yanzu babu wanda ke da masaniya kan takamaimai kwayoyin cutar dake haddasa cutar daji a jikin mutum amma bincike ya nuna cewa kwayoyin cutar HPV ne ke haddasa kashi 14% na cutar a jikin mutum.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce nau’ukan kwayoyin cutar HPV 16 da 18 ne ke haddasa kashi 70% na cutar dajin dake kama mahaifa.
Kungiyar ta Kuma ce HPV na haddasa dajin dake kama al’auran namiji da mace, nono, dubura da dai sauran su.
WHO ta ce za a iya dakile yaduwar cutar idan aka yi wa kashi 90% na mata allurar rigakafi, kashi 70% na mata na gwajin cutar sannan akalla kashi 90% na mata na samun maganin cutar.
Malaman addini da sarakunan gargajiya
Shuaib ya yi kira ga malaman addini da su hada hannu da gwamnati wajen inganta fannin lafiyar kasar nan.
“Malaman addini na da mahimmiyar rawar da za su taka wajen wayar da kan mutane sanin mahimmancin yin allurar rigakafin cutar da kawar da duk wani canfi da mutane ke yi akan cutar da ke hana su yin rigakafin.
A karshe, shugabannin addinai sun bayyana goyon bayan su akan haka.
Discussion about this post