Fitacciyar ƴar jam’iyyar APC a Kaduna Bilkisu Gidado ta yi kira ga ƴaƴan Jam’iyyar da su daina ruruta wutan tashon hankali tsakanin ƴaƴan jam’iyyar a jihar.
Da take zantawa da manema labarai a garin Kaduna, kamar yadda Tribune ta buga, Bilkisu ta karyata cewa wai gwamnan jihar yi adawa da zaɓin tsohon gwamna Nasir El-Rufai na Ja’afaru Sani ya musanya shi a kujerar minista.
Ta karyata raɗeraɗin cewa wai gwamna Uba Sani, ma so a canja Jaafaru Sani da Yusuf Hamisu Mai Rago a kujerar minista.
Bilkisu ta ce, Ja’afaru Sani, da Yusuf Mairago duk sun bauta wa APC a jihar kuma duk wanda ya zama minista cikin su ɗaya ne, babu banbanci.
A karshe ta yi kira ga ƴaƴan jam’iyyar su ci gaba da ba jam’iyyar haɗin kai domin samun nasarar ta.
An yi zargin cewa gwamna Sani ya nuna rashin amincewar sa da zaɓin Ja’afaru Sani da El-Rufai ya yi, an buga cewa gwamna Uba Sani a fusace ya garzaya fadar Tinubu inda ya ce bai amince da haka ba, shi Hamisu Mairago ya ke so.
Sai da kuma, gwamnan ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa ba maganar minista ya kai shi fadar ba.
” Ba gaskiya bane wai na yi adawa da zaɓin El-Rufai, ana neman a haɗa mu yamutdi ne kawai.”
Discussion about this post