Kakakin rundunar ‘Yan sandan Kano Mohammad Gumel ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama barayin waya, Yan Kwalewa da tantiran ‘yan iska da batagari a fadain jihar ranar Litinin.
Gumel ya ce dukka wadanda aka kama an tattara su ne daga tsakiyar watan jiya zuwa wannan mako.
Ya ce daga cikin bata garin da rundunar ta kama akwai ‘yan fashi 117, masu garkuwa da mutane 25, masu safarar mutane guda 17, barayin shanu 6, barayin babura 26, barayin waya 28, ‘Yan Kwalewa 34 da barayin Keke Napep.
Gumel ya ce rundunar za ta kai wadannan mutane kotu domin a yanke musu hukunci.
Gumel ya yi kira ga mutane da su ci gaba da mara wa rundunar baya domin ganin an kawo karshen ayyukan batagari a kasar nan.
Discussion about this post