Dalibai ‘yan Najeriya dake karatu a kasar Niger na kokawa da yadda dole su ka dakatar ka karatun su a dalilin matsalolin juyin mulki da sojoji suka yi a kasar.
Kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar Nijar takunkumin diflomasiyya, da ya sa mutanen kasar ke fama da matsanancin rugujewar tattalin arziki da kuma matsi na rayuwa.
Wata daliba dake karatun aikin asibiti a jami’ar Maryam Abacha Maradi mai suna Aisha Suleiman ta shiga halin damuwa matuka a dalilin juyin mulki da aka yi a kasar Nijar da kuma takunkumin da aka saka wa kasar.
“Fargabana shine shekarun da na yi ina karatu ya zama na banza da a yanzu haka baza mu iya shiga kasar ba sannan idan ma ka shiga akwai kiyayya tsakanin mu da ‘yan kasa saboda barazanar afka wa kasar yaki da ECOWAS ta ke shirin yi da suke ganin kamar Najeriya ce ke ruruta wutar haka.
Shima Abdurrashid El-Ladan Bakatsine dake karatu a jami’iar Maryam Abacha ya koka da irin haka.
Hauwa Usman-Shehu mai shekara 19 da kanwarta Fatima Usman-Shehu mai shekara 18 dake karatu a jami’ar Abubakar Ibrahim a Maradi sun ce matsalar juyin mulkin ya shafe su matuka, domin karatun su ya tsaya cak yanzu.
Da yawa da ga cikin daliban sun koka cewa yanzu suna cikin damuwa. Ba su san ranar da za a dawo karatu ba sannan kuma ba a san makomar karatun su ba ko bayan an samu maslaha da gwamnatin soja dake kasar.
Akwai jami’o’i da dama mallakin ‘yan Najeriya dake kasar Nijar da ‘Yan Najeriya da dama suke karatu a cikin sa. Juyin mulkin da ka yi, da kuma takunkumin da ka kakaba wa kasar Nijar, zai iya kawo musu koma baya a harkar ilimi da kuma gudanar da karatun su.
Discussion about this post