‘Yan bindiga sun sako sauran manoma 56 da suka yi garkuwa da su daga kauyukan Kafin Koro da Kwagana dake karamar hukumar Paikoro a jihar Niger.
Idan ba a manta ba ‘Daily Nigerian’ ta buga labarin cewa a ranar 14 ga Maris ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 60 daga kauyen Kafin Koro da kauyukan dake kusa da shi.
Mafi yawan mutanen da aka yi garkuwa da su manoma ne.
Maharan sun saki wasu mutane daga cikin yawan da suka yi garkuwa da su bayan ‘yan uwansu sun biya kudin fansan su.
Sai dai a watan Yuni maharan sun saki wani bidiyo inda suke barazanar cewa za su kashe sauran mutanen dake hannunsu idan har ba a biya kudaden fansan su ba.
Kodinaton kungiyar matasan Kaffin-Koro Sabastine Maikarfi ya ce maharan sun sako mutum 56 ranar 6 ga Agusta.
Maikarfi ya ce maharan sun saki wadannan mutane bayan da aka biya kudin fansan su.
Kodinatan kungiyar inganta shari’a, ci gaba da zaman lafiya na cocin darikan Katolika dake Minna Rev. Fr Bahago Dauda-Musa ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen Samar da likitocin da za su kula da mutanen da aka sako ganin cewa da dama daga cikinsu na fama da ciwon damuwa, da kuma zautuwa.
Discussion about this post