‘Yan bindiga sun kashe mutum uku sannan sun yi garkuwa da wasu mutum 13 a kauyen Mayanci dake karamar hukumar Maru jihar Zamfara ranar Litinin wannan makon.
Mazauna kauyen sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun dauki tsawon sa’o’I biyu suna barna a kauyen.
Wani mazaunin kauyen Badaru Mayanci da yake bayani ranar Talata ya ce maharan sun kashe tsohon shugaban jami’yyar APC na mazabar Mayanci Dahiru Maizabura da wasu, Isuhu Nana da Umar Gurmu.
“Maharan sun ajiye baburansu a wani wuri sannan suka shigo kauyen a kafa kafin karfe 12 na dare suna harbi da ko ina.
Ya ce maharan sun yi wa mazan dake hira a teburin mai shayi a Fakon Idi diran mikiya domin mutanen da suka ji harbin bindiga sun zaci na ‘yan banga ne.
Wani Usman mazaunin kauyen ya ce maharan sun kashe Dahiru Maizabura a cikin shagonsa.
“Shagon Maizabura na wani bangaren daban daga kauyen inda da ya ji harbin bindiga sai ya yi kokarin arcewa amma maharan suka harbe shi kafin ya gudu.
Ya ce sauran mutane biyu da maharan suka harbe sun gamu da ajalinsu yayin da suke tsaye a kofar gidajen su a daidai za su gudu.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan banga.
Mayanci ya ce maharan sun yi garkuwa da wasu daga cikin ‘yan bangan dake kauyen.
“Mace daya ce maharan suka kama tare da maza sai dai bayan wani dan lokaci kadan sai a ka ga ta dawo sun sake ta, Matar tana da tsohon ciki ba za ta iya dogon tafiya ba.
Discussion about this post