‘Yan bindiga sun kashe wasu malaman makarantar sakandaren ‘Beco Comprehensive High’ a Kwi dake karamar hukumar Riyom jihar Filato ranar Litini da misalin karfe uku na rana.
Maharan sun kashe Rwang Danladi da matarsa Sandra Danladi Wanda a kwanakin baya suka yi aure kuma sun ji wa mataimakin Shugaban makarantar Dalyop Emmanuel Ibrahim rauni.
Shugaban kungiyar matasan Berom BYM Rwang Tengwong da ya sanar da haka ranar Talata ya ce maharan sun kashe wadannan malamai yayin da suke tattauna shirye-shiryen da za su yi taron yaye daliban makarantar da za a yi ranar Juma’a mai zuwa.
Kungiyar na zargin Fulani makiyaya ne suka kashe malaman.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Alabo Alfred bai ce komai ba game da abin da ya faru.
Wannan hari ya auku kwanaki biyar da ‘yan bindiga suka kashe mutum 21 a karamar hukumar Barikin Ladi
Gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya yi Allah wadai da wannan kisa, sannan ya umarci jami’an tsaro su gaggauta kamo wadanda suka aikata wannan mummunar abu.
Tengwong ya ce a ranar Litini da misalin karfe uku na rana wasu Fulani makiyaya sun shigo harabar makarantar da shanun su, bayan malaman makarantar sun kore su sai kawai suka buda musu wuta da bindigogi.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta saka dokar hana kiwon dabbobi a a ko ina.
Bayan haka Shugaban kungiyar Miyetti Allah MACBAN Garba Abdullahi ya musanta cewa fulani makiyaya ne suka kai harin amma ya yi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike domin kamo wadanda suka kai harin.
Discussion about this post