Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa gwamnati ta ware kudade domin tallafa wa talakawan jihar domin rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.
A bayanin da ya yi gwamna Sani ya ce gwamnati ta raba yadda za a raba tallafin ga talakawan jihar zuwa rukuni uku kamar haka:
A. Raba abinci ga takalawa da gajiyayyu.
B. Inganta fannin sufuri domin samar da ababen hawan da za su rika ɗaukan mutane a farashi mai sauki tare da tallafa wa manoma da masu kananan sana’o’in hannu.
C. Farfado da jiragen kasa da za su rikan ɗaukan mutane daga Zaria zuwa Kaduna da kuma daga Sabon Tasha zuwa Kafanchan.
Gwamna Sani ya ce a rukunin farko gwamnati za ta raba abinci wa mutum miliyan 1,050,000 da suka hada da tsofaffi, zaurawa, da marayu a jihar.
“Gwamnati za ta raba wa gidajen talakawa buhunan shinkafa 43,000.
“Gwamnati za ta kafa kwamitin da za ta shugabanci raba abincin inda mambobin kwamitin suka hada da shugabanin kananan hukumomin jihar, matasa, kungiyar kwadago, ma’aikatan kananan hukumomin, kungiyar mata, malaman addini da kungiyoyi masu zaman kan su.
Daga nan sai gwamna ya yi kira ga mutane da su ba gwamnati hadin kai domin samun nasarar wannan aiki na raba tallafi.
A karshe gwamna Sani ya gargaɗi waɗanda za su yi wannan aiki da wadanda za su mori wannan tallafi kada su kuskura su yi sama da fadi da kayan abinci da aka bada a raba, yana mai cewa duk wanda aka kama zai ɗyaba wa aya zaki.
Discussion about this post