‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 12 da a cikin su akwai wata mata maijego daga kananan hukumomin Ningi da Toro a jihar Bauchi.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa maharan sun afka wadannan kananan hukumomi a daren Asabar din da ta gabata.
Jaridar ta samu labarin cewa maijegon da aka yi garkuwa da ita sunan ta Adama Abdulsalam mai shekaru 20 kuma mijinta dan kasuwa ne a Yadagungume dake karamar hukumar Ningi.
A karamar hukumar Toro wani mazaunin kauyen Gumau Musa Adamu ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Babangida Danrimi da Saleh Jange daga kauyen su.
“ Hankalin mutanen kauyen ya tashi matuka ganin yadda hare-haren ‘yan bindigan ya dawo gadan-gadan a yankin. Ya kawo mana cikas a harkokin kasuwancin mu.
Wani basarake a karamar hukumar Ningi Manu Garba ya ce maharan sun yi garkuwa da mutum shida a kauyen Yadagungume da cikin su akwai wata mata mai jego da jaririnta.
Garba ya ce maharan sun ci gaba da kawo musu hari bayan kwanaki 16 da jami’an tsaro suka dakile su.
Ya ce tun bayan wadannan kwanaki maharan sun kai wa kauyuka uku hari a cikin kwanaki uku a karamar hukumar.
Wani mazaunin karamar hukumar da baya so a fadi sunnan sa saboda tsaro ya ce a ranar Alhamis din da ta gabata ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum daya a kauyen Sanger dake karamar hukumar Kwangoro.
Ya ce maharan sun kira iyalen wanda suka tafi da shi sun bukaci a biya su kudin fansa.
Mutumin ya ce a daren Alhamis ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Chibi Lumbu da Sibs Lumbu a Billiri Gorore a karamar hukumar Lumbu.
Discussion about this post