‘Yan bindiga sanye da hijabi a ranar Litinin sun yi garkuwa da wani dan kasuwa mai suna Alhaji Isiya a Maru, jihar Zamfara.
Maharan bisa babura uku sun dira ƙauyen Hayi, da nan ne Isiya ke zaune da misalin karfe 10 na daren Litinin.
Alhaji Isiya babban dan kasuwa ne da ya shahara wajen siyar sa zinari.
“Maharan sun yi gaggawar aecewa da Isiya a lokacin da suka yi garkuwa da shi domin gudun kada jami’an tsaro su cimma su.
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an ga maharan tare da Isiya suna tafiya amma daga nan ba a sake ganin sa ba.
Sai dai kuma an shaida cewa tuni jami’an tsaro sun fantsama neman sa domin ceto shi da kuma mako maharan da suka sace shi
Discussion about this post