A ranar Litinin ce Amurka ta aika da tawaga zuwa Jamhuriyar Nijar, a ƙarƙashin Mataimakiyar Sakataren Harkokin Waje ta Riƙo, Victoria Nuland.
Sai dai buƙatar Amurka ta ƙoƙarin ganawa da hamɓararren Shugaban Ƙasa, Mohammed Bazoum da Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdourahmane Tchiani bai yi nasara ba.
Duk da haka, tawagar Nuland ta gana da wasu jiga-jigan juyin mulki, a ƙarƙashin Janar Moussa Barmou, wanda shi ne Babban Hafsan Tsaron Nijar, tare da wasu Kanar-kanar guda uku.
Nuland ta shaida cewa ba ta samu ganawa da Shugaban Mulkin Soja ko hamɓararren Shugaban Ƙasa, Bazoum ba.
Da ta ke magana da manema labarai na duniya ta wayar tarho daga Yamai, kafin ta bar ƙasar, Nuland ta ce sun nemi su gana da Bazoum, domin duba lafiya, walwala da jin daɗin sa. Amma aka hana ta ganawa da shi, kamar yadda aka hana ta ganawa da Shugaban Mulkin Soja, Janar Abdourahmane Tchiani.
‘Ta Wayar Tarho Kaɗai Na Yi Magana Da Bazoum’ – Nuland:
“Mun samu yin magana da Bazoum ta wayar tarho, amma ba mu gan shi ba. Sai da kawai mu ka hana tsawon sa’o’i biyu da Janar Moussa Barmou.”
Sauran mutanen da Victoria Nuland ta gana da su, sun haɗa da ƙungiyoyin kare haƙƙi daban-daban na cikin Nijar, ‘yan jarida, da ‘yan kishin dimokraɗiyya.
Sojojin Amurka A Nijar:
Aƙalla akwai sojojin Amurka 1,100 a cikin Nijar, saboda Bazoum ya ƙulla dangantaka da Shugaba Joe Biden na Amurka, musamman a ɓangaren yaƙi da ta’addanci.
Nijar ce ƙasa na cikin ƙasashe 10 da ta’addanci ya yi wa kaka-gida a duniya.
Shi kuwa Janar Barmou da ya gana da tawagar Amurka, ya yi aiki shekaru da dama a baya tare da Sojojin Musamman na Amurka da ke Nijar.
Nuland ta ce hakan ya ba su damar ganawa da Barmou tsawon lokaci, domin su fahimci juna.
‘Amurka Ba Ta So Nijar Ta Tattago ‘Yan Ta-kifen Dakarun Wagner Group’ – Nuland:
Victoria Nuland ta sanar da cewa, “a zaman da mu ka yi da Barmou, sun fahimci barazanar da Nijar ka iya afkawa idan ta tattago sojojin haya na Wagner Group.
“Amma ba cewa na yi ina da yaƙinin Nijar na tunanin tattago sojojin haya na Wagner Group ba.” Inji Nuland.
Ta ce ta nemi su bar wa juna ƙofofin tattaunawa a buɗe, domin ƙasar ta koma bisa turbar dimokraɗiyya a cikin lalama.
Discussion about this post