Dakarun Najeriya sun ceto daya daga cikin ‘yan matan Chibok da aka yi garkuwa da su a shekarar 2014.
Kodinatan yaki da ta’addanci a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Tanimu Musa ya ce dakarun sun ceto Rebecca Kabu ranar 17 ga Yuli a kasar Kamaru.
Musa ya bayyana wa uwar gidan Shugaban kasa Oluremi Tinubu cewa Boko Haram sun yi garkuwa da Rebecca tana da shekaru 13 a shekarar 2014, a yanzu ta cika shekara 22 a duniya.
Ya ce likitoci sun tabbatar cewa Rabecca na cikin koshin lafiya sannan nan ba da dadewa ba za ta koma gida wajen iyayenta a kauyen Zana.
Musa ya ce ofishin NSA za ta hada Rabecca da sauran ƴan matan Chibok 15 da aka ceto domin gwamnatin tarayya ta dauki nauyin karatunsu na boko.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda a zamanin mulkin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan Boko Haram suka yi garkuwa da daliban makarantar sakandare a Chibok jihar Borno a shekarar 2014.
Zuwa yanzu Sojojin Najeriya sun ceto mafi yawan ƴan matan da Boko Haram suka yi garkuwa da su.
Uwargidan Shugaban kasa Oluremi Tinubu ta ce za ta yi kokari wajen ganin Rebecca ta samu taimakon da za ta bukata domin ci gaba da karatun ta.
Discussion about this post