Wani helikwaftan Sojojin Saman Najeriya ɗauke da sojojin da suka jikkata, ya faɗi a kusa da ƙauyen Chukuba, ranar Litinin, a Jihar Neja.
Jirgin samfurin MI-171, ya bar makarantar Firamare ta Zungeru ɗauke da wasu sojojin da aka jikkata, domin ya garzaya da su Asibitin Sojoji a Kaduna.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya shaida a cikin wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai cewa, sun gano jirgin ya yi hatsari kusa da ƙauyen Chukuba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro, a Jihar Neja.
Ya ce ana ƙoƙarin ceto matuƙan jirgin da sauran waɗanda ke cikin sa, bayan ya faɗi ƙarfe 1 na ranar Litinin.
Haka nan kuma ya ce an fara binciken musabbabin faruwar hatsarin.
Jihar Neja na fama da dandazon ‘yan ta’addar da aka tabbatar cewa Boko Haram ne. Sannan kuma jiha ce da ‘yan bindiga su ka yi wa kaka-gida a cikin dazuka daban-daban, musamman a dazukan yankin Birnin Gwari.
Yankin Shiroro kuma an haƙƙaƙe cewa Boko Haram ne maƙil a cikin sa.
Discussion about this post