Wata mata mai wa’azi kuma Shugaban cocin ‘Liberty Gospel’ dake Calabar jihar Rivers Helen Ukpabio ta bayyana yadda wani dan sanda ya tsare ta a hanya ya tilasta ta bashi cin hancin man fetur lita 15.
Helen wace ta sanar da haka a shafinta na ‘Facebook’ ta ce dan sandan ya tsayar da ita a hanyar Ogoni ranar Lahadin da ya gabata yayin da take hanyar dawowa daga Fatakwal za ta Calabar inda take zama.
Ta ce ta yi sama da awa daya suna gwagwa da sandan sai ta bashi cin hanci.
“Ni bana bada cin hanci. Ta ce.
Helen ta ce a dalilin rashin bada cin hancin ne dan sandan wanda ke rike da bindiga kirar AK-47 ya fara caje jakan ta da cikin mota.
“Dan sandan ya sa na bude jakata sannan don mugunta ya zubar da kayan dake ciki ko zai samu kudi.
Hellen ta Saka hotuna da bidiyon minti daya da sakan bakwai na yadda dan sanda ke caje mata jaka.
Sai dai kuma a bidiyon ba a ji lokacin da dan sandan ke tambayan a bashi cin hancin ba.
Discussion about this post