Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da sakataren aiyuka na jami’iyyar APC Kawu Yakassai.
Maharan sun sace Yakassai ranar Juma’a a gidan sa dake karamar hukumar Soba a jihar Kaduna.
Mai taimaka wa gwamnan jihar Uba Sani kan harkokin yada labarai Mohammed Shehu bayan ya sanar da haka ya ce gwamna Uba ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta ceto Yakassai tare da kamo waɗannan mahara.
“Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta mai da hankali matuka wajen yakan rashin tsaro a jihar.
“Daga cikin matakan samar da tsaron da gwamnati ta dauka shine daukan matasa 7,000 aikin ‘yan sa kai domin karfafa aiyukan tsaro a jihar.
Discussion about this post