1. Jamhuriyar Nijar ta fi Najeriya faɗin ƙasa nesa ba kusa ba. Amma kuma a yawan al’umma, Najeriya ta nunka Nijar kusan sau goma. Yawan ‘yan Najeriya a ƙididdigar 2023 ya haura miliyan 225, su kuma al’ummar Nijar ba su wuce miliyan 27 ba.
2. Nijar ta haɗa kan iyaka da Katsina, Zamfara, Sokoto, Barno.
3. Nijar ta haɗa kan iyaka da ƙasashen Aljeriya, Libya, Chadi, Nijeriya, Benin, Burkina Faso, Mali da Najeriya.
3. Nijar ta riga Najeriya samun ‘yanci da tazarar watanni biyu. Na ta ‘yancin a ranar 1 Ga Agusta, 1960, iya kuma Najeriya ranar 1 Oktoba, 1960.
Auratayya:
4. Idan ka ɗauka kama daga Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Jigawa har zuwa Barno, Allah kaɗai ya san yawan auratayyar da ake yi tsakanin Najeriya da Nijar a duk shekara.
5. Attajirai, manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya, na jihohi da ƙananan hukumomi, manyan ‘yan siyasa, hatta gwamnoni, sanatoci, ‘yan majalisa akwai auratayya sosai tsakanin wasun su da Nijar.
A cikin Abuja yanzu haka ba a san yawan matan Nijar masu auren masu mulki na da can da yanzu da ke a kai ba.
6. A Kano kaɗai akwai miliyoyin mata da mazan Nijar kama daga kakanni, iyaye da ‘ya’yan su da asalin su daga Nijar ne, amma haihuwar Najeriya.
7. Garuruwa irin su Daura da maƙwautan su kuwa, yaudarar kai ne idan wani ɗan Najeriya ya yi ƙoƙarin raba su da Nijar.
Zamantakewa Tsakanin Najeriya Da Nijar:
8. Yawanci ƙauyukan kan iyakokin mu da Nijar babu wata iyakar da ta raba mu. Idan ka shiga wasu garuruwan, za ga cewa ko dai kwalta ce ta raba garin zuwa Najeriya da Nijar, ko layi, ko shararra, ko kwalbati ko doguwar magudanar ruwa. Amma cure ake a wuri ɗaya.
Mu’amalar Kasuwanci Tsakanin Najeriya Da Nijar:
9. Matsawar aka samu tangarɗa ko tasgaro ko wani cikas a kan iyakokin ƙasashen biyu, to Najeriya da Nijar kowa zai afka cikin matsanancin ƙuncin rayuwa.
10. A yanzu haka Allah kaɗai ya san iyar yawan dukiyar ‘yan Nijar a kasuwannin Kano, musamman Kantin Kwari.
11. Haka kuma Allah kaɗai ya san iyakan dukiyar ‘yan kasuwar Arewa da ke kara-kainar shiga da fita zuwa Nijar ko shigowa Najeriya daga Nijar.
12. Yawancin kasuwannin ƙauyukan Najeriya da ke maƙautaka da Nijar duk tare da juna ake hada-hada a cikin su.
13. Dubban ‘yan Arewa musamman daga Kano da maƙwauta sai hijira su ke yi su na komawa da harkokin kasuwancin su zuwa cikin manyan garuruwan Nijar. Maginan zamani, kanikawan motoci masu tsada, telolin zamani, kafintocin zamani, masu gyaran wuta da sauran ayyukan fasahar amfani da hannu ko ƙarfi, sai tafiya ake yi ana buɗe hada-hada a manyan biranen Nijar.
13. Ko shakka babu, ƙarin ƙarfin arziki da kasuwancin Kano, ya dogara ne da hada-hadar shigo da kaya ko saye a fita da su waje, daga Kano zuwa Nijar da wasu ƙasashe.
14. Kenan su ma kayan da ake sayarwa a kasuwannin Kano, yawanci ta kan iyakokin Nijar ake shiga Kano da su.
15. Za ka iya yin la’akari da yawan mutanen da jami’an kwastan na Najeriya ke kashewa idan sun shigo da buhunan shinkafa a sukwane daga cikin Nijar.
16. Da dama na ganin cewa idan yaƙi ya ɓarke, zai koma tsakanin Arewa ce da Nijar kawai, domin duk wata hada-hadar kasuwanci da cinikayya da bunƙasa, ba za su samu tawaya ko cikas a Legas ba.
Discussion about this post