Hukumar kula da tsaftace muhalli na Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta rusa wata kasuwa mai suna ‘Kasuwar Dare’ a Abuja.
Gwamnati ta rusa wannan kasuwa dake layin Hassan Usman Katsina kusa da Kpaduma II a Asokoro saboda yadda wurin ya zama matattarar ‘yan kwaya da ƴan iska.
A zantawarsa da NAN, Daraktan sashen kula da ci gaba ta FCTA, Mukhtar Galadima, ya ce kasuwar na zama barazana ga mazauna yankin.
Ya ce an mayar da yankin mafakar aikata muggan aiyuka duk da kokarin da hukumar babban birnin tarayya ke yi na gyara wurin.
“Rusa kasuwar zai taimaka wajen kawar da ‘yan iska da masu sayar da muggan kwayoyi da suka mamaye kasuwar. Wannan shine karo na uku da muke rusa wurin amma sai su koma daga baya su gine wurin.
“A wannan karon kasuwar muka rusa Kuma za ta ci gaba da zama a rushe. Muna buƙatar tsaftace wurin kuma mu haɓaka kyawun yanayin muhalli.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne hukumar FCTA ta rusa wani katafaren gida mai lamba 226 Cadastral Zone, A02 Wuse 1, dake Wuse 6, saboda saɓa dokar yin gini.’
Galadima, ya ce ginin na Marigayi Alake Landan Egba, Oba Oye Lipede ne, amma Ibrahim Kamba da Adamu Teku suka kwace wurin sannan suka gina wannan katafaren gini duk da gargaddin kada a yi da gwamnati ta rika yi musu.
Galadima ya ce FCTA ba za yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk wani dake Kokarin kawo koma baya a ci gaban da gwamnati ke samu a aikin da ta saka a gaba.
Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce zai rusa duk wani ginin da aka yi ba bisa ka’ida ba a Abuja.
Discussion about this post