An sake kama daga cikinin ministocin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa sunayen su a majalisa da laifin giribtun katin shaidar NYSC.
Yanzu haka Olubunmi Tunji-Ojo ya shiga tsomomuwar tababar sahihancin katin sa na shaidar aikin yi wa ƙasa hidima, wato NYSC, wanda ya gabatar wa Majalisar Dattawa, domin ta tantance shi.
PREMIUM TIMES kafin shi, ta buga labarin yadda Hannatu Musawa da aka tantance ita ma a shekarun baya Majalisar Dattawa ta ƙi tantance ta lokacin da gwamnatin Buhari ta nemi naɗa ta wani muƙami. A lokacin sai dai aka maye gurbin ta da sunan wani.
An ƙi tantance Hannatu a lokacin Buhari, saboda kwamitin Sanata Shekarau ya gano cewa ba ta yi NUSC ba, kuma ta kasa bayyana dalilin hakan.
Amma yayin da Tunji Ojo ya bayyana a Majalisar Dattawa ranar Talata, sai Sanata Sadiq Umar mai wakiltar Kwara ta Arewa, ya takalo wasu bambance-bambance a cikin katin shaidar NYSC na Ojo ɗin.
Umar ya nemi sanin dalilin da ya sa Ojo ya yi NYSC ya na ɗan shekara 37, kamar yadda katin shaidar ya nuna? Kuma me ya sa ranar da aka rubuta cewa ya kammala NYSC ɗin akwai ruɗani a cikin ta?
“Ka sani nan fa Majalisar Dattawan Najeriya ce. Mu na so mu tabbatar cewa mun yi aikin ƙwarai sosai wajen tantance ka.” Cewar Sanata Umar.
Ojo ya amsa masa da cewa ai wanda ya kammala jami’a zai iya zuwa bautar ƙasa ko da bayan shekara nawa ne, matsawar dai ya kammala jam’iyar kafin ya cika shekaru 30. To haka ya ce shi ɗin ma ya yi.
Shi dai Ojo ya ce ya kammala NYSC cikin 2020. Amma kuma ya karɓi satifiket na kammala NYSC a cikin watan Fabrairu, 2023.
Hakan ya sa akwai nauyi kan Ojo ya bayyana jihar da ya yi aikin bautar ƙasa, sansanin da ya sauka da sauran hujjojin da za su tabbatar da ya yi aikin NYSC ɗin.
Takardun Ojo dai sun nuna cewa ya kammala digiri na farko a shekarar 2005, a London Metropolitan University, ya na ɗan shekara 23.
Binciken da PREMIUM TIMES ta yi kan katin shaidar NYSC na Ojo, ya nuna akwai mishkiloli har biyu, yayin da ta gwada shi da na waɗanda su ka kammala shekara ɗaya da shi Ojo ɗin ya ce ya kammala.
Haka kuma babu sunan sa a jerin sunayen waɗanda suka kammala shekara da zango ko rukunin da shi ya ce ya kammala NYSC ɗin sa.
PREMIUM TIMES ta kira Ojo bai ɗauka ba, kuma ta aika masa da saƙon tes, bai amsa ba.
Sai dai Kakakin NYSC, Eddy Megwa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun fara bincike. Kuma za su bayyana sakamako ba da daɗewa ba.
Discussion about this post