A jihar Anambra ne Wani limamin Coci mai shekaru 30 Prosper Igboke ya kashe kan sa saboda budurwarsa ta ci amanar sa.
Bisa ga rohotan wanda ‘Punch’ ta buga marigayi Igboke ya kashe kan sa bayan ya nemi budurwar sa da suka daɗe ta aure sa amma ta ki.
Wannan abu ya faru a kauyen Nnewi dake karamar hukumar Nnewi ta Arewa, jihar Anambra.
Wani dan uwan mamacin da baya so a fadi sunnan sa ya bayyana wa manema labarai ranar Asabar cewa mamacin dan asalin kauyen Leru ne dake karamar hukumar Umunneochi amma bayan ya zama fasto sai ya dawo da zama kauyen Nnewi domin aikin Fasto.
“A lokacin da yake aiki a kauyen ne ya hadu da wannan yarinya kuma kai tsaye ya yi mata tayin soyayyar sa. Daga nan sai dauki nauyin karatun ta tun daga lokacin.
Mutumin ya ce su Iyamurai kan yi haka musamman idan suna son yarinya da aure.
“Sai dai a ranar Asabar bayan wannan yarinya ta kammala karatunta na jami’a sai ya kai mata ziyara gida domin taya ta murnar kammala karatu lafiya, amma ta botsare masa ta ce ba kaunar sa kuma.
Fitan shi daga gidan wannan yarinya sai ya hau wani bene can saman benen ya faɗo kasa.
“Mun jefar da gawar sa a can cikin daji ranar Juma’a, ba mu birne shi saboda abin da ya aikata ya saba wa al’adun mu.
” Ban taɓa tsammanin Igboke zai aikata haka ba duba ga shekarunsa da matsayinsa na fasto.
Discussion about this post