Wasu tubabbun ‘yan Boko Haram sun yi zanga-zanga a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno, su na zargin cewa gwamnati ta bar su cikin yunwa da rashin kulawa.
Sun yi zanga-zangar a ranar Juma’a, a Maiduguri, daidai lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa a Najeriya.
Aƙalla ‘yan Boko Haram 6,900 ne su ka tuba, tare da miƙa wuya ga jami’an tsaro, bayan sun bayyana yin watsi da aƙidar ta’addanci.
Tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin dai sun ɓalle daga Sansanin Alhazai na Maiduguri, inda ake masu horon zama mutane nagari, daga nan su ka shiga zanga-zanga a kan titina, su na neman sai Gwamnati ta biya su alawus ɗin Naira 30,000 ɗin ta yi alƙawarin za ta riƙa biyan kowanen su a duk wata.
Wannan zanga-zanga dai ta haifar da razana, fargaba da matsanancin cinkoson motoci a kan hanyar Bulunkutu zuwa Maiduguri, kafin jami’an tsaro su je su kwantar da matsalar.
Tubabbun Boko Haram ɗin sun ce tilas ce ta sa su fitowa su shaida wa duniya ƙorafin yin watsi da su da Gwamnati ta yi, saboda an bar su babu wadataccen abinci kuma babu kulawa.
Sun ce gwamnati ta yi masu alƙawarin farfaɗo da su tare da maida su cikin al’umma su ci gaba da rayuwar neman halaliyar su.
Da ya ke magana dangane da lamarin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Usman Tar, ya ce, “an ci gaba da aikin tantance tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin bayan wannan zanga-zangar.
“Bayan komai ya lafa, jami’an Gwamnatin Jihar Barno sun ci gaba da aikin tantance tubabbun ‘yan Boko Haram ɗin.
“Akwai tubabbun ‘yan Boko Haram 6,900 da ke ƙarƙashin Shirin Amshe Makamai, Tuba, Wayar Da Kai, Sasantawa da Sake Tsugunarwa (DDDRRR), wato Shirin ‘Borno Model”, inji Kwamishina Tar.
Ya ce an tsara gudanar da tantancewar a kashi shida, wanda wasu ƙwararrun ICT da jami’ai ke yi, domin a killace bayanan kowane daga cikin su.
Ya ce an samu ɗan cikas ne, wanda ya haifar da ruɗani a cikin sansanin da su ke a killace.
“Gwamnatin Jihar Barno na tabbatar da cewa yanzu an shawo kan lamarin a wurin da ake yin aikin tantancewar.
Discussion about this post