Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya shaida cewa Rundunar Sojojin za ta ci gaba da shirya horaswa ga zaratan ta, domin ƙara zaburas da su wajen ƙara zage damtse su fuskanci ayyukan da ke gaban su.
Lagbaja ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke jawabin buɗe taron kwana ɗaya da Rundunar Sojojin Dibijin na 6 da ke Fatakwal ya shirya, a ranar Laraba.
Taron mai take: Ƙara Zaburas Da Zaratan Sojojin Najeriya, Kawar Da Damuwa Da Daƙile Tu’ammali Da Muggan Ƙwayoyi’.
Lagbaja ya ce ƙasar nan ta na fuskantar matsaloli da ƙalubale na tsaro daban-daban, waɗanda suka haifar da ɗora wa sojoji nauyin daƙile waɗannan matsaloli da ƙalubale.
Ya ce domin ganin an cimma biyan buƙatar magance matsalolin, Sojojin Najeriya za su sake nazarin salo, dabaru, fasaha da tsare-tsaren yadda za a ga bayan mugaye, maɓarnata da abokan gaba.
“Abin damuwa matuƙa a gare mu, ganin yadda tu’ammali da ƙwayoyi masu bugarwa ke ƙasa tasiri a cikin sojojin Najeriya. Sai kuma matsalar Tsananin Damuwa Bayan Kasancewa a Filin Daga, wato PTSD.
“Wannan damuwar ce ta sa za mu wayar wa da sojoji kai dangane da illar tu’ammali da ƙwayoyi masu bugarwa da kuma magance damuwar da wasu zaratan mu ke fuskanta, domin mu ƙara zaburas da su.
Ya ce nauyin kwamandojin sojojin Najeriya ne su ƙara wa zaratan su ƙaimi ta hanyar ƙara masu caji, ƙaimi, tsima su da kuma ƙara cusa masu ɗa’a.
Discussion about this post