Yayin da Najeriya ke tsakiyar fama da ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sai kuma Boko Haram, Shugaba Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasiƙar sanar da su matakan da ECOWAS ta ɗauka domin tabbatar da an dawo da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar.
Cikin wasiƙar wadda ke ɗauke da sanarwar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar, waɗanda har wasu sun fara aiki, har da shirye-shiryen ɗaukar matakin yin amfani da ƙarfin soja, domin a ƙwatar wa hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum mulkin sa daga hannun sojoji.
Akwai matakan datse wutar lantarki a Nijar daga wutar lantarki, sai kuma dakatar da shigar da kaya daga Najeriya da ƙasashen ECOWAS zuwa cikin Nijar.
Sai dai kuma labarin baya-bayan nan ya tabbatar da cewa Nijar ta yanke hulɗa da Najeriya, bayan tattaunawa tsakanin sojojin mulkin ƙasar da tawagar shiga tsakanin ECOWAS da Nijar a ƙarƙashin tsohon Shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ta tashi baram-baram.
PREMIUM TIMES ta ruwaito Bazoum ya ce tsige shi zai haifar wa Nijar, ECOWAS, Afrika da duniya gagarimar matsala
Discussion about this post