Ko shakka babu sojojin Jamhuriyar Nijar sun tattago wa kan su rikicin da bai dace su jefa ƙasar a ciki ba.
Sun rungumi juyin mulki a daidai lokacin da shugabannin ECOWAS, AU da duniya ake ƙara ƙyamar mulkin soja, kuma daidai lokacin da sabon Shugaban ECOWAS Bola Tinubu ke ta ƙara jaddada cewa yankin ba zai sake amincewa da mulkin soja ba.
Saboda haka kifar da gwamnatin farar hula a cikin wannan yanayi tamkar tsokanar faɗa ne tsakanin ɓera da giwa.
Auratayya Tsakanin Najeriya Da Nijar:
Duk da cewa akwai mata masu aure Nijar masu yawa daga Najeriya, to wannan yaƙi zai haifar wa Nijar janyewar mu’amalar auratayya, za a kusan daina tsallakawa ana auro matan su.
Zamantakewa Tsakanin Najeriya Da Nijar:
Kusan rabin Nijar su na mu’amala da Najeriya a kowace rana. Katse hulɗar kasuwanci, shiga da fita da sauran takunkumi ba zai yi wa Nijar da al’ummar ƙasar daɗi ba.
Haka kawai sojojin ƙasar su na neman jefa ƙasar su a yaƙin da ba su da ƙarfin yin nasara a kai.
ECOWAS a ƙarƙashin Bola Tinubu dai ta nuna da gaske ta yi, sai fa idan an samu hanyar sasantawa a cikin ruwan sanyi.
Goyon bayan da Nijar ke samu daga Mali, Burkina Faso da Gini tabbas ya rage ƙumajin ECOWAS. Sai dai kuma Hausawa sun ce Sarkin Yawa, ya fi Sarkin ƙarfi, ballantana su huɗu da na su ƙarfin ko kashi 30 bisa 100.
ECOWAS na da dalilin ƙoƙarin ganin ko ta halin ƙaƙa farar hula sun koma mulkin Nijar, domin abin da ya ci Doma, ba ya barin Awe.
Yayin da Mali, Gini, Burkina Faso, Chadi da kuma ta biyar Nijar ke ƙarƙashin mulkin soja kuma a cikin ECOWAS, wannan babbar barazana ce ga manya da ƙananan ƙasashen cikin ƙungiyar, ciki kuwa har da Najeriya, Ghana, Saliyo, Togo da Benin da Senegal da Gambiya.
Ƙara Dagula Matsalar Tsaro A Nijar:
Juyin mulkin Nijar zai haifar wa ƙasar wata sabuwar matsalar tsaro, bayan wadda a yanzu su ma su ke fama da ita a ƙasar.
Hamɓaras da gwamnatin dimokraɗiyya babban laifi ne mai janyo wa ƙasa da al’ummar ta koma-baya.
Babban haɗari ne a ce saboda giyar mulki sojojin Nijar su jefa ƙasar cikin tashin hankali, saboda shugabanci.
Ina Amfanin Juyin Mulkin Da Zai Jefa Nijar Cikin Raɗaɗin Tsadar Rayuwa:
Duk girman ƙasa da ƙasaitar ta, idan aka sa mata takunkumi, sai ta tagayyara. Shin me ake tunani zai kasance a Nijar idan aka ƙaƙaba mata takunkumi?
Duk yadda rayuwa ta yi tsada yanzu a Najeriya, to a Nijar abin ya fi muni. Sake shiga wani mawuyacin halin kuwa, laifin sojojin juyin mulki ne.
Discussion about this post