Shugaban kasa Bola Tinubu zai nada Atiku Bagudu minista, mutumin da ya taimakawa tsohon shugaban kasa marigayi Sani Abacha sata da wawure biliyoyin daloli na Najeriya.
Bagudu, mai shekaru 61, dan majalisar tarayya ne kafin ya yi gwamnan jihar Kebbi na tsawon shekaru takwas. Mutum ne wanda ya yi fice a jam’iyyar APC kuma aminin shugaban kasa Tinubu ne na kud da kud a siyasance.
Sai dai kuma a lokacin mulkin Abacha, Tinubu da Bagudu ba aminan juna bane Hasali ma, a lokacin da Bagudu ke taimakon Abacha, suna wawuce dukiyar Najeriya, Tinubu a nashi ɓangaren adawa yake da gwamnatin, inda ya rika taratsi da shiga gaba wajen yin zanga-zanga nuna kiyayya ga gwamnatin soja na Abacha, abinda ya sa dole ya yi gudun hijira zuwa kasar waje saboda fargabar gwamnatin a wancan lokaci na bibiyar rayuwar sa.
Sai dai kuma da Tinubu da Bagudu sun dunkule wuri guda bayan kafa jam’iyyar APC, inda dukkan su ke ƴaƴan jam’iyyar.
Kusantar su ya kara karfi a lokacin zaben 2023, inda Bagudu ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ganin Tinubu ya yi nasara a zaɓe wanda ya yi.
An rika bankaɗo harƙalla masu dama wanda Bagudu ke da hannu a cikin su dumudumu a lokacin mulkin janar Abacha.
Har yanzu gwamnatin Najeriya na ci gaba da kwato miliyoyin daloli da Abacha ya jibge a kasashen waje a lokacin sa.
Discussion about this post