Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya, kungiyar ECOWAS ta aika da tawaga ta musamman domin ganawa da gwamnatin sojoji da su ka yi juyin mulki a Nijar, domin a samu sulhu.
Wadanda aka tura wa wannan tawaga sun kunshi sarkin Musulmi, Dr Sa’ad Abubakar da tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar.
Sai dai kuma wannan tawaga ba ta samu tarba mai daɗi ba.
Tun daga saukar su filin jirgin kasar Nijar, wakilin gwamnatin soji dake mulki a kasar ya tarbe su amma bai bari sun shiga cikin kasar ba sai aka ajiye su a wani ɗaki a filin jirgin.
Janar Moussa Barmou, ya shaoda wa tawagar cewa dalilin tsaro ya sa ba za a bari su shiga cikin kasar ba.
Nan dai aka barsu zaune zuru-zuru ba a ce musu komai ba, har sai ranar Juma’a da dare, aka ce musu su koma Najeriya kawai ba za su iya ganawa da shugaban mulkin Soja na kasar ba.
Wannan shine tawaga na uku da ECOWAS da Najeriya ke aikawa domin ganin an shawo kan abin, sojoji su yarda koma bariki, shugaban kasa Mohammed Bazoum ya koma kan mulkin sa.
Gwamnatin Soji na Nijar ta sha alwashin ba za ta dawo da Bazoum ba, kuma a shirye ta ke fafata da duk kasar da ta nemi ta kawo mata matsala a wannan juyin mulki da suka yi.
Discussion about this post