Masu Sana’a cikin garin Zaria da ma wasu makwabtan jihohi sun sami halarta taron ranar masu sana’a ta Duniya,rashen yankin Zazzau karo na biyu.
Taron wanda ya gabata a ranar Lahadi,anyi shine a dakin karantarwa na sashin koyar da aikin kananan hukumomi dake jami’ar Ahmadu Bello a kongo Zariya.
Daya daga cikin masu jawabi a taron,wato Dr Umar Sani Bebeji esq.,ya yi kira da masu sana’a suyi kokarin bin doka da tsarin fara sana’a din gujewa fadawa matsala.Yayi nuni da cewa,kar mai sana’a ya saka hannu a kowani irin yarjejeniya da wasu,ba tare da ya nema lauya da zai mishi fashin baki ba.
Shima Shugaban Kamfanin Dogaro da kai Hub,da ke Kano,wato Badamasi Aliyu yayi tsokaci ne kan yadda masu sana’a ya kamata su rike shi hannu bibbiyu,tare da amfani da kafafen yaɗa zumunta wurin talllata su.
A bangaren manyan baƙi kuwa,Mai girma wakilin Birnin Zazzau,Suleiman Ibrahim Dabo yayi kira da a rinka bibiyar mahalarta irin wannan taron,don ganin sun aiwatar da abinda suka koya.
A wurin taron dai,an samar da wurin baje koli ga masu sana’a, don tallata hajojin su ga mahalarta.
Tun da farko shugaban shirya taro,wanda shine shugaban kamfanin BYY innovations dake Zariya, Bello Yusuf Yusuf,ya nuna godiya da jin dadi yadda bayan tsawon lokaci na shirye-shirye,taron ya samu nasara.Ya kara da godiya ga manya baki da suka tattaki daga wurare daban-daban don zuwa wayar ma ‘yan uwa masu sana’a kai,don a gudu tare,a kuma tsira tare.
Muhammad Kabir(MK Global services),na cikin wanda suka zo daga garin Kaduna don halartar taron,kuma ya nuna gamsuwa da taron.
Mahalarta sun tashi taro cikin farin ciki da annushuwa,tare da fatan Allah ya kai mu na shekara mai zuwa.
Discussion about this post