Da wahala taron baya-bayan da Shugabannin ECOWAS ke yi a Abuja su yanke shawarar afka wa Nijar da yaƙin ƙwato dimokraɗiyya, ganin yadda alamu ke nuna cewa shugabannin za su ƙara bada ratar lokacin ci gaba da neman sulhu da mahukuntan Nijar.
Dalili shi ne, Shugaban ECOWAS kuma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida wa sauran shugabannin yankin cewa su ƙara yin amfani da hanyoyin sasanci da hukumomin mulkin sojan Nijar.
“Muna nan kan bakan mu na jaddada dimokraɗiyya, kare ‘yancin ɗan Adam, da kiyaye rayuwar al’ummar Nijar.
To sai dai kuma ƙungiyoyi da shugabannin addinin Musulunci da Majalisar Dattawa da sauran ‘yan Najeriya waɗanda ba su so a yi yaƙi, su na cewa idan aka yi yaƙi, ai al’ummar Nijar ce za a kashe, kuma a ƙara talauta su, maimakon ƙarajin ceto su da ECOWAS ke cewa.
A jawabin sa wurin taron ECOWAS na ranar yau Alhamis, ya ce har yanzu su na tare da Shugaban Nijar na farar hula da ke tsare, Mohammed Bazoum.
Sannan kuma su na Allah-wadai da juyin mulkin Nijar wanda sojoji su ka yi.
Haka kuma Tinubu ya ce ba su yarda da ci gaba da tsare Bazoum ba, wanda zaɓaɓɓen shugaba ne wanda farar hula ta zaɓa bisa turbar dimokraɗiyya.
Bayan Tinubu ya yi masu tariyar abubuwan da suka faru tsawon sati ɗaya bayan ayyana wa’adi da kuma bayan cikar wa’adi, ya ce har yanzu su na nan kan bakan su na sojojin Nijar su sauka su bayar da mulki ga wanda su ka karɓa a hannun sa.
Sai dai kuma ya ce ya fi kyau a ci gaba da bin lamarin ta hanyar lalama har a kai ga sulhuntawa ta hanyar tuntuɓar ɓangarorin biyu.
“Ta haka za a gamsar da su fa’idar sauka su sake ɗora Bazoum a kan mulki.
“Haƙƙin mu ne mu tuntuɓi hanyoyin da suka dace domin tabbatar da maida dimokraɗiyya bisa gurbin ta a Jamhuriyar Nijar.
A ƙarshe Tinubu ya yi nuni da cewa tilas su yarda cewa matsalar rikita-rikitar mulki a Nijar bazarana ce ba ga Nijar kaɗai ba, har ma ga Afrika ta Yamma baki ɗaya.
Discussion about this post