Daga 1975, shekarar da aka kafa ƙungiyar ECOWAS mai ƙasashe 15 zuwa 2023, an yi juyin mulkin da aka yi nasara da waɗanda ba a yi nasara ba, jimillar 126.
A tarihin Afrika ta Yamma, an fara juyin mulki a ƙasar Togo, cikin 1963, a ranar 13 Ga Janairu.
Shekaru uku bayan na Togo, sai sojoji su ka yi wa gwamnatin farar hula ta Tafawa Ɓalewa juyin mulki mafi muni, a ranar 15 Ga Janairu, 1966.
Daga 1952 idan aka yi ƙididdiga, za a ga cewa an yi juyin mulki sau 10 a Burkina Faso, sau 9 a Gini Bisau, sau 8 a Mali, sau 10 a Saliyo, sannan sau 10 a Ghana.
A Jamhuriyar Benin an yi juyin mulki sau 8, a Jamhuriyar Nijar can ma sau 8, haka a Najeriya an yi sau takwas, amma na cikin 9, na Gidieon Orkar bai yi nasara ba. A ƙasar Chadi an yi juyin mulki sau 7.
Kai a tarihin juyin mulki a Afrika ta Yamma, ƙasashen Sanagal da Cape Verde ne kaɗai ba su taɓa ɗanɗana shi ba.
Shi kan sa jagoran tawagar ECOWAS wanda ke shiga tsakanin ECOWAS da Sojojin Mulkin Nijar, wato Abdulsalami Abubakar, tsohon soja ne da ya taɓa yin mulkin watanni 9 a Najeriya.
Kafin sannan kuwa, akwai shi a juyin mulkin da aka yi wa farar hula zamanin Shehu Shagari, da shi aka yi wa Buhari juyin mulki, da hannun shi a juyin mulkin Janar Sani Abacha ya yi wa gwamnatin riƙon ƙwarya. Sannan kuma shi ne ya yi Shugaban Mulkin Soja bayan rasuwar Abacha.
Idan aka kamfato har cikin sauran ƙasashen Afrika kuwa, za a ga cewa a Sudan an yi juyin mulki sau 17, a Burundi sau 11, sai a Tsibirin Comoros kuma an yi juyin mulki sau 8.
Afrika ta Yamma, yanki ne wanda gaba ɗayan masu zaɓe a Najeriya sun haura yawan masu zaɓe a sauran ƙasashen ECOWAS 14 ɗin.
Za a ga cewa mafi yawan ƙasashe masu neman a Afka wa Nijar da yaƙi, ƙasashe ne da su ma sun taɓa kasancewa a ƙarƙashin mulkin soja, ba sau ɗaya ko sau biyu ba.
To kuma wasu ƙasashen na ECOWAS, dimokmurɗiyya su ke yi ba dimokraɗiyya ba. A Kamaru dai Paul Biya ya shafe shekaru 40 ya na mulki. Rashin lafiya ta sa ya tafi neman magani, amma kuma ya wakilta ɗan sa kan mulki, kafin ya koma.
Wasu ƙasashen masu rajin dimokraɗiyya kuma ana ƙorafin cewa ba sahihin zaɓe ake yi ba, sai dai ƙarfa-ƙarfa da ɗauki-ɗora, a zaɓukan da ko da yaushe ake ƙoƙarin cewa an yi maguɗi.
A Najeriya dukkan zaɓukan da aka gudanar daga 1999 har zuwa 2023 babu wanda ba a yi ƙorafin yin maguɗi ba.
Dalili kenan tun daga kan tsoffin Shugabannin Ƙasa irin su Olusegun Obasanjo, Umaru Yar’adua, Goodluck Jonathan, Buhari duk sai da aka dangana Kotun Koli kafin a tabbatar da cancantar nasarar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓe.
Goodluck Jonathan ne kaɗai ya haƙura bai je kotu ba a zaɓen 2015, wanda Muhammadu Buhari ya kayar da shi.
Shi kan sa Shugaban ECOWAS na yanzu, Bola Tinubu, ‘yan takara huɗu ne su ka ƙi amincewa da nasarar da ya samu. Amma dai a yanzu haka akwai shari’a biyu da ya ke ta gwagwagwa a kan ta, tsakanin sa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, waɗanda su ka jayayya ko su ka ƙi yarda da sahihancin nasarar da INEC ta ce Tinubu ya samu, a zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
Jama’a da dama na ganin cewa ita Najeriya ita kan ta dimokraɗiyya ta rage karsashi, ganin cewa fiye da mutum miliyan 93 suka rajistar katin zaɓe, amma wanda ya zo na ɗaya yawan ƙuri’un sa ko miliyan 10 ba su kai ba.
Manyan ‘yan takara uku, Tinubu, Atiku da Obi, har ma da Kwankwaso wanda ya zo na uku, yawan ƙuri’un su ba su kai miliyan 30 ba.
Juyin mulkin Nijar, wanda ko kaza sojoji ba su kashe wajen aiwatar da shi ba, to zai yi wuya jama’a su goyi bayan a kai hari a ƙasar don a ƙwace shi da ƙarfin tsiya, a yaƙin da ba wanda zai ce ga adadin mutanen da za su iya rasa rayukan su.
Discussion about this post