A ranar Lahadi ce bayan Sallar Isha’i, ‘yan bindiga su ka yi awon gaba da mutum 19 a ƙauyen Madogara, cikin Ƙaramar Hukumar Batsari, a Jihar Katsina.
Yawancin waɗanda aka yi garkuwa da su dai mata ne, har su 16, sai kuma maza 3. Ko da yake kuma an tabbatar da cewa wasu matan su na ɗauke da jarirai da ƙananan yara a lokacin da aka yi gaba da su zuwa cikin Dajin Rugu.
Wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa “dama saboda tsoron kai hare-hare a ƙauyen, sai mazauna gidajen da ke gefen gari su riƙa shigowa su na kwana cikin wasu gidaje uku da ke a tsakiyar ƙauyen, a kullum dare. Sai da safe idan gari ya waye duk su koma gidajen su.”
Majiyar ta ce maharan sun yi samame bayan Sallar Isha’i su ka dira ɗaya daga cikin maɓuyar mutanen ƙauyen.
Ya ƙara da cewa sun shiga ƙauyen ba tare da yin harbi ko sau ɗaya ba, don kada jama’a su farga da su. Kuma don kada harbin ya jawo hankalin jami’an tsaron da ke kusa da ƙauyen, a kusa da wani ƙauye da ake kira Nahuta.
“An tafi da ƙanuwa ta da ‘ya’yan ta biyu.” Haka wani mai suna Sadiq Hamisu ya shaida wa wakilin mu, wanda ya ce maharan sun dira garin daidai lokacin da suka kammala Sallar Isha’i.
“Sun shigo garin a lokacin da babu wanda ya taɓa tunanin za su iya shigowa a daidai lokacin.”
Shi ma wani mai suna Aminu Lawal ya ce an tafi da ‘yan uwan sa.
“An tafi da matar kawu na da anti na. Kowacen su an tafi da ita da ‘ya’yan ta. Mun dai lissafa mutum 19 da aka tafi da su, kuma har yanzu ba su kira kowa ba ta wayar tarho balle a ji miradin su.”
Ya ƙara da cewa wani ƙarin abin takaicin da su ke fuskanta, shi ne yadda saboda tsaro ko gona ba su iya zuwa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Abubakar Sadik cewa ya yi a ɗan ba shi lokaci domin ya tabbatar da sahihancin kai harin.
Idan ba a manta ba a yankin ne dai ‘yan bindiga su ka jidi manoma da dama a ƙauyukan Nahuta, Madogara, Ɗantsuntsu, Zamfarawa da Dadare. Kuma har yanzu su ɗin ma ba a sako su ba.
Discussion about this post