Babban Hafsan Sojojin Sama, Hassan Abubakar, ya bayyana cewa Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta yi odar jiragen helikwafta na yaƙi guda 18, domin ƙara yawan jiragen ta na yaƙi.
Abubakar ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar kwana ɗaya a rundunonin da ke ƙarƙashin NAF 115, masu Ayyukan Musamman, ranar Laraba, a Fatakwal.
Ya ce Amurka za ta kawo jirage 12, yayin da saura guda shida kuma Gwamnatin Turkiyya ce za ta aiko da su a cikin watan Satumba.
“Ba mu yi ƙasa a guiwa ko nuna sarewa ba dangane da abubuwan da su ka faru kwanan nan. Saboda Gwamnatin Tarayya ta amince mu sayo ƙarin jirage 12 samfurin AH1 Zulu Cobra, daga Amurka. Akwai kuma wasu guda shida samfurin T129 ƙasar Turkiyya.
“Cikin Satumba za a kawo guda biyu samfurin T129 daga Turkiyya.
“Lallai mun ji baƙin cikin yin asarar jirgin mu ɗaya samfurin MI 171, wanda ya yi hatsari a Jihar Neja. Amma wasu da yawa na nan tafe, domin ƙara yawan waɗanda mu ke da su.” Cewar sa.
Abubakar ya ce ya je Jihar Fatakwal ce domin ya yi wa iyalan Sojojin Saman da suka rasa rayukan su ta’aziyya.
“Bayan ta’aziyya ga iyalan su, kuma mun zo domin ƙarin ƙwarin guiwa ga Sojojin Operation Delta Safe.”
A ranar 14 Ga Agusta ne helikwaftan Sojojin Saman Najeriya ya faɗo ƙasa, jim kaɗan bayan ɗagawar sa sama, ɗauke da sojojin da suka jikkata sanadiyyar wani gumurzu da ‘yan ta’adda a yankin Shiroro cikin Jihar Neja.
Kwana ɗaya bayan hatsarin jirgin ne kuma aka watsa wani bidiyon da ke nuna ‘yan bindiga yaran Gogarma Dogo Giɗe kewaye da jirgin, su na iƙirarin cewa su ne suka kakkaɓo shi.
Bayan kwana uku kuma Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta yi asarar sojoji 36 a wani kwanton ɓauna da ‘yan ta’adda su ka yi masu a yankin Shiroro na Jihar Neja.
Discussion about this post