Mahukuntan Sojojin Najeriya sun bayyana wasu ‘yan Najeriya masu kiraye-kirayen a yi juyin mulki, cewa marasa kishin ƙasa ne, kuma mugaye.
Kakakin Yaɗa Labaran Sojojin, Tukur Gusau ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai a ranar Asabar.
Tukur wanda Burgediya Janar ne, ya jaddada cewa Rundunar Sojojin na goyon bayan dimokraɗiyya 100 bisa 100.
“Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta nuna ɓacin rai matuƙa dangane da wani rahoton da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya mai danganta cewa Sojojin Najeriya na fama da matsalar rashin ba su kyakkyawar kulawar da ta cancanta.
“Rahoton dai har kira ya yi ga sojoji su kawar da mulkin dimokraɗiyya, wanda hakan kuwa rashin kishi ne da mugunta, da kuma ƙoƙarin kawar da hankalin sojojin Najeriya daga gudanar da aikin su, wanda dokar ƙasa ta wajibta masu.
“Yayin da Shugabannin Hafsoshin Sojojin Najeriya na ƙoƙarin su wajen kyautata kulawa ga ɗaukacin sojojin Najeriya, to kuma mun yi tofin tir ga duk wani guruf ko mutumin da ke ƙoƙarin ingiza Sojojin Najeriya masu biyayya ga dokokin ƙasa cewa wai su kawar da gwamnati.
“Mun fito ƙarara mu na ƙara faɗin cewa Sojojin sun fi farin ciki da samun kulawa a ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya. Don haka ba za mu sa kai cikin duk wata maƙarƙashiyar da za ta kawo zagon-ƙasa ya dimokraɗiyya a ƙasar nan ba.
Sojojin Najeriya a ƙarƙashin Babban Hafsan Tsaron Ƙasa Janar CG Musa, a shirye su ke domin yin aiki a ƙarƙashin mulkin dimokraɗiyya a cikin biyayya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Kuma ba za a iya karkatar da hankulan su daga yin biyayya ga wannan tsari ba, kamar yadda Dokar Ƙasa ta 1999 ta shar’anta masu.”
Haka Tukur ya kammala sanarwar, wadda ya roƙi a watsa ta sosai a kafafen yaɗa labarai.
Discussion about this post