Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 36 sannan sun kama wasu 163 a cikin makonnin biyu da suka gabata.
Darektan yada labarai Edward Buba ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya ce dakarun sun kama ‘yan bindiga 137, masu siyar da bindigogi da harsasai uku, sun ceto mutum hudu da aka yi garkuwa da su, sun kama mutum 12 dake hada baki da ‘yan bindiga da barayin man fetur guda 15,
Ya ce dakarun sun kama har da kudi naira miliyan 3.1, sun ceto mutum 140 da aka yi garkuwa da su, bindigogi 37 da harsasai 370.
“Daga cikin makaman da dakarun suka kama akwai bindigogi kirar AK-47 guda 16, bindiga kiran Pump action guda 6, bindigogi kirar hannu uku, kananan bindigogi biyu da harsasai da dama.
“Dakarun sun kuma kama motoci 8, babura 45, wayoyin salula 32, adduna 925 da dutsen wasa adda guda 151.
Buba ya ce dakarun sun ragargaza rijiyoyon mai 61, kwalekwale 32, tankunan mai 87, jirgin ruwa daya, murhun girki guda 32, jenereto daya, na’uran tsatso mai guda biyu, na’uran Outboard guda uku da matatun mai 36.
Ya ce dakarun sun kama lita 310,700 na bakin mai, lita 14,675 na AGO, lita 49,000 na kalanzir da lita biyar na man fetur.
A Arewa maso Gabas Buba ya ce ‘Opertion Hadin Kai’ sun kashe ƴan ta’adda 9 sannan sun kama wasu guda 19, mutum shida dake hada baki da ‘yan bindiga, sannan sun ceto mutum 12 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce ‘yan ta’adda 313 da suka hada da maza 12, mata 138 da yara 162 sun mika wuya.
Rundunar sojin sama ta kashe ‘yan ta’adda da dama a harin da suka kai sansanin maharan dake Wulade.
A Arewa ta Tsakiya Buba ya ce ‘Operations Safe Haven da Operation Whirl Stoke’ sun kashe ‘yan ta’adda da dama a jihohin Benue, Nasarawa, Filato da Taraba.
Ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven’ sun kama AK-47 2, bindiga hannu uku, harsasai da damai.
“Bincike ya nuna cewa daya daga cikin manyan bindigogi kiran AK-47 da dakarun suka kama na korarren sojan ne dake aiki tare da ‘yan bindiga.
A Arewa maso Yamma Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su sannan ta kama wasu ‘yan ta’adda a kananan hukumomin Jibia, Matazu da Funtua jihar Katsina.
Buba ya ce ‘Operation Whirl Punch’ sun kama masu hada baki da ‘yan bindiga da masu siyo wa maharan kaya a kasuwa, sun ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su, sun kama makamai da dama a kananan hukumomin Chikun da Kajuru jihar Kaduna.
“Dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 11, kama bindigogi biyu kirar hannu, harsasai masu yawa da babura 3, da kuma kaji 80.
“Jami’an tsaron sun kama ‘yan ta’ada da masu hada baki da ‘yan bindiga 16 sannan sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su.
Discussion about this post