Dakarun sojin Najeriya dake karkashin ‘1Division’ sun kashe ‘yan bindiga uku sannan sun kama mahara da dama a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
Daga cikin makaman da dakarun suka kama akwai bindiga kirar AK 47 daya, bindigogi kirar hannu biyu, harsasai da babura takwas.
Saura sun hada da harsasai, wayoyin hannu guda shida , muggan kwayoyi da layu.
Shugaban rundunar ‘1Division’ Kuma Shugaban rundunar ‘Operation Whirl Punch’ BA Alabi ya jinjina namijin kokarin jami’an tsaron sannan ya hore su da su kara kaimi domin kawo karshen ta’addanci a jihar Kaduna.
Discussion about this post