Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi alkawarin kawo sauye sauye ma su ma’ana a jam’iyyar APC.
Hakan na kunshe ne a jawabin sa bayan amincewa da naɗin sa shugaban APC da majalisar zartaswar APC ta yi a Abuja ranar Alhamis.
Majalisar zartaswar Jam’iyyar APC ta tabbatar da Ganduje da Ajibola Bashiru a matsayin shugaban jam’iyyar kuma sakataren jam’iyyar na kasa a safiyar ranar Alhamis.
Tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, da sakataren jam’iyyar na kasa, Iyiola Omisore, a watan jiya, sun yi murabus daga shigabancin jam’iyyar.
Da yake jawabi bayan tabbatar da shi, Ganduje ya kuma yi alkawarin fara yin garambawul a cikin jam’iyyar don daidaitawa da “yanayin siyasa na yanzu”.
” Babban abin da za mu mayar da hankali a kai shi ne inganta hadin kan jam’iyya da da kara yawan kujerun siyasa da muke da su a halin yanzu.
” A karkashin mulki na, APC za ɗau saiti, sannan za mu tabbatar an samu haɗin kai da karfin guiwa a tsakanin ƴaƴan jam’iyyar duka.
“Za a gudanar da wasu gyare-gyare a jam’iyyar daidai da yanayin siyasar da ake ciki,” in ji shi.
A karshe ya yi kira ga ƴaƴan jam’iyyar a Jihohin Imo, Kogi da Bayelsa da za a gudanar da zaɓen gwamna da na ƴan majalisar dokokin jihohin da su hada kawunan su a yi tafiya tare domin samun nasara a zaɓukan.
Discussion about this post