Ƙungiyar ECOWAS ta umarci sojojin ta su ɗaura ɗamarar yaki da tsirarun sojin da suka yi juyin mulki a Nijar domin dawo ceto dimokuraɗiyya a Nijar.
Shugaban majalisar ECOWAS Omar Touray ya ce duk hanyoyin da aka bi domin samun sulhu da sojojin da suka yi juyin mulki ya ci tura a dalilin haka dole a tunkare su da karfin soja kawai don a kauda su.
A dalilin haka, ECOWAS ta umarci manyan hafsoshin tsaron kasashen yankin su fara kimtsawa domin kakkaɓe waɗanda suka yi juyin mulki a Nijar a dawo da zaɓaɓɓiyar gwamnati da jama’ar kasar suka zaɓa.
Discussion about this post