Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Shugaban ta bayyana cewa nan gaba za ta bayyana ranar da za ta yanke hukuncin ƙarar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ya kai Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen, Haruna Tsammani ne ya bayyana hakan a ranar Talata, cewa za a sanar wa ɓangarorin biyu ranar da za a yanke hukuncin.
Atiku ya maka Tinubu, APC da INEC kotu, inda ya ƙalubalaci nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa.
A zaman kotun na ranar Talata, lauyan INEC Abubakar Mahmoud ya roƙi kotu ta yi watsi da ƙarar da Atikun ya shigar, domin a cewar sa, babu wasu hujjojin da shi Atiku ɗin ya bayar.
Lauyan INEC ya ce an samu nasara wajen amfani da na’urorin BVAS da IReV a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce “‘yar matsalar da ta faru yayin loda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, tsawon sa’o’i huɗu da minti 50 kacal.”
Haka kuma ya ce tattara sakamakon zaɓe da aka yi da hannu ba da na’ura a wasu wurare, ai bai dagula sakamakon zaɓen ba.
Shi ma lauyan Tinubu wato Wole Olanipekun, cewa ya yi tattare sakamakon zaɓen ba da na’ura ba, bai rage masa sahihanci ba.
Ita ma APC ta roƙi kotu ta yi fatali da roƙon da Atiku ya yi mata, domin ya kasa gabatar da hujjoji da zai tabbatar da shi ne ya yi nasara, da kuma maguɗin da ya ke cewa an yi masa.
Tunda an kammala sauraren ɓangarori, za a yanke hukunci kafin ranar 16 Satumba.
Discussion about this post