Ƙungiyar Kare Haƙƙi ta SERAP, ta garzaya kotu, inda ta shigar da ƙarar neman a hana kashe wa Sanatoci da Mambobin Tarayya zunzurutun kudi har Naira biliyan 110 domin a sai masu jibga-jibgan motoci masu sulke.
“SERAP na so kotu ta hana Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Tarayya, Tajuddeen Abbas, a hana su karɓar Naira biliyan 40, domin sayen motoci masu sulke guda 465.
SERAP ta ce cire kuɗin ba ya cikin dokokin Najeriya, don haka cire su a lodo motoci asara ce, kuma haram ne.
Haka kuma sun ce Naira biliyan 70 da aka ce za a raba wa majalisa kuɗaɗen tallafi, ita ma doka ba ta bayar da iznin ba su tallafin ba.
Shigar da ƙarar na zuwa daidai lokacin da Sanata Akpabio ya raba wa Sanatoci sama da naira miliyan 200.
SERAP ta maka su ne Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, kuma ta na son a rage Kasafin Majalisa da Naira biliyan 110, duba da la’akari da halin matsin tattalin arziki da raɗaɗin tsadar rayuwar da ake ciki.
Cikin ƙarar dai SERAP ta ce ‘yan Najeriya na da ‘yancin su nemi a riƙa ririta kuɗaɗen gwamnati, ta hanyar hana masu riƙe da muƙamai ɗirka satar kuɗaɗen da hana su yin almubazzaranci da dukiyar al’umma.
SERAP ta nuna damuwa cewa yayin da za a kashe wa sabbin ‘yan Majalisar Tarayya Naira biliyan 70 su 306, amma ‘yan Najeriya sama mutum miliyan 200 za a kashe masu tallafin Naira biliyan 500. A hakan ma, mutum miliyan 12 ne kaɗai za su ci moriyar tallafin na marasa galihu.
Lauyoyi biyu, Kolawole Oluwadare da Blessing Ogwuche su ka shigar da ƙarar a madadin ƙungiyar.
Discussion about this post