Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh
Ya ‘yan uwana Zamfarawa masu albarka, ya kamata mu sani, da shi Dauda Lawal da ya zama Gwamnan jihar Zamfara da shi Bello Muhammad Matawalle da ya zama Ministan Najeriya duk wannan daga Allah ne, cikin su ba wanda ya ba kansa wannan matsayi. Babu wanda wayonsa ne ko dabararsa ya bashi. Munyi imani da Allah, a matsayin mu na Musulmi cewa, Allah shine yake bayar da mulki da matsayi ga wanda yaso. Don haka, ya zama tilas, wajibi kuma dole muyi masu addu’a dukkaninsu, muyi masu fatan alkhairi, Allah ya basu sa’a, Allah yasa suci nasara, Allah yasa ace gwamma da aka yi. Allah yasa su zamar wa jihar Zamfara alkhairi da Najeriya baki daya, kuma Allah ya fitar da su kunyar duniya da ta lahira, amin.
Amma mutum ya koma gefe yana soke-soke da zage-zage da cin mutunci; ko ya kasance yana rubuce-rubucen banza a social media, ko ya shiga rediyo ko talabijin yana babatun banza, don yana goyon bayan Gwamna ko yana goyon bayan Minista, to wallahi duk wannan bai yi ba, kuma bai dace ba, kuma a matsayin mu na Musulmi, mu sani, wannan haramun ne, haramun ne, haramun ne!
Duk mai kishin jihar Zamfara da Najeriya da gaske, duk mai son a samar da tsaro da ci gaba da kwanciyar hankali, to kamata yayi ya dage da addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala yasa wadannan shugabanni su zama alkhairi a gare mu baki daya.
Don haka ina kira da muji tsoron Allah, muyi masu addu’a, muyi wa jihar mu da kasar mu addu’a.
Duk siyasar da muke yi, mu tuna cewa mu Musulmi ne, mu al’ummah ce musulma. Don haka shi Musulmi yana da dokoki da ka’idodin da suke yi masa jagoranci a cikin dukkanin rayuwarsa, ba haka kawai yake rayuwa sagaga ba! A tare da shi akwai mala’iku masu rubuta duk abunda yayi, na sharri ko na alkhairi.
Sannan su kuma wadannan shugabanni guda biyu, wato da shi Gwamna Dauda Lawal da kuma shi Minista Muhammad Bello Matawalle, ina rokon su, ina kiran su, da suji tsoron Allah Subhanahu wa Ta’ala. Su sani cewa, su jarabawa ne da Allah ya jarrabi Zamfarawa da su. Don haka, ya zama wajibi su hada kai domin su kawo wa jihar Zamfara da Najeriya baki daya alkhairi da ci gaban da zai amfani kowa da kowa. Kar su yarda su zama sharri ga al’ummarsu. Suyi kokari su zama alkhairi a garesu. Kar su yarda da masu zuga, kar su yarda da ‘yan-bani-na-iya, ‘yan kanzagi, masu banbadanci, wadanda su a koda yaushe, fadan shugabanni da rigimarsu da hayaniyarsu shine hanyar cin abincinsu. Irin wadannan mutane, wallahi babu wani alkhairi a tare da su sai sharri.
Gwamna Dauda Lawal, Minista Muhammad Bello Matawalle, ku sani, ku biyu din nan, Allah zai tashe ku a gabansa, a filin alkiyama, domin yi maku hisabi akan wannan jagoranci da ya dora maku. A wannan rana wallahi babu wani magoyi bayan ku da zai iya fitar da ku illa ayukkanku da kuka gabatar. Don haka, kar ku taba yarda da zugar wani magoyi baya, wanda sam a ranar lahira ta kan sa yake yi, kuma kuna ta kan ku. Don haka don Allah ku kiyaye.
Wallahi kaunar da nike yi maku tsakanina da Allah, da kuma kishi na ga jiha ta da kasa ta, shi yasa na rubuta wannan sako mai albarka. Domin ina kallon duk abunda yake faruwa kuma yake gudana a jiharmu. Idan lamarin yaci gaba a haka to tabbas, jiharmu da al’ummarmu dama ku kan ku, ba za kuji dadi ba.
Ku manta da maganar banbancin jam’iyyar da ke tsakaninku, ku manta da banbancin siyasar da ke tsakaninku, kuji tsoron mahaliccinku, ku kalli al’ummarku, kuyi kokari ku hada kai domin tunkarar rashin tsaro da yunwa da talaucin da suke addabar jiharmu ta Zamfara mai albarka.
Muhammad Bello Matawalle, a matsayin da Allah ya baka na Ministan tsaro, ya zama tilas, in dai kana son tsira a gaban Allah, ka hada kai da Gwamna Dauda Lawal, kuyi aiki tare, domin samar da kyakkyawar natija.
Gwamna Dauda Lawal, a matsayin ka na Gwamnan jihar Zamfara, wanda Allah ya damka amanar tsaron jihar Zamfara da ci gabanta, da zaman lafiyarta a hannunka, kai ma ya zama tilas, in dai kana son tsira a gaban Allah, ka hada kai da Minista Muhammad Bello Matawalle, kuyi aiki tare, ba tare hangen wani banbaci na jam’iyya ko na siyasa ba, domin kawo wa jihar Zamfara da ma Najeriya baki daya ci gaba.
Wannan shine gaskiyar magana, wadda duk wani masoyinku na gaskiya, wannan ya kamata ya gaya maku. Duk wanda zai gaya maku akasin haka, duk wanda zai zuga ku domin ku zama makiyan juna, to ku sani, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, wannan mutum ko waye shi, to ba masoyinku bane. Makiyin kune, wanda yake so ya jefa ku cikin rame, ya bar ku da jangwam a gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala.
Sannan dukkanin manyan ‘yan siyasarmu na jihar Zamfara suma ya zama dole su mayar da hankali wurin zamar wa jihar Zamfara da Najeriya baki daya alkhairi: irin su mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, mai girma tsohon Gwamna Sanata Abdul-Aziz Yari, mai girma tsohon Sanata Marafa, mai girma Dan Majalisa Aminu Sani Jaji, mai girma Sanata Ikra Aliyu Bilbis, mai girma Sanata Sahabi Ya’u Kaura, mai girma Dan Majalisa Kabiru Amadu Mai Palace, kI da duk ma wadanda ban ambata ba, dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar siyasar jihar Zamfara, ya zama wajibi a gare mu da muji tsoron Allah, mu zama alkhairi ga jihar mu mai albarka.
Gaskiyar magana ita ce, dukkaninku kuna da magoya baya, kuna da masoya, akwai dimbin jama’ar da suke bayanku, don haka wuka da nama duk a hannunku suke. Idan kun gyara kun sani, kuma idan kun bata kun sani.
Sannan duk wanda yayi da kyau, ya sani, Allah zai yaba, kuma al’ummah zasu yaba. Duk kuma wanda ya bata, to ya sani, zai jawo wa kansa fushin Allah, kuma al’ummah zasu yi Allah waddai da shi.
Allah yasa mu dace, ya ganar da mu, amin.
Daga dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau. Juma’ah, 18/08/2023. 08038289761.
Discussion about this post