Sabon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nysome Wike, ya ce kafin ya karɓi tayin minista sai da ya nemi amincewar wasu shugabannin PDP tukunna.
Wike wanda shi ne Gwamnan Jihar Ribas wanda ya sauka cikin Mayu, ɗan PDP da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).
An rantsar da shi tare da sauran dukkan ministocin da Tinubu ya naɗa a ranar Litinin.
Sai dai naɗin da aka yi wa Wike ya jawo ce-ce-ku-ce, ganin cewa shi ɗan PDP ne, sannan kuma ya taɓa cewa ya fi ƙarfin ya rage darajar sa ya koma ya yi minista bayan ya kammala shekara takwas a matsayin gwamna.
A taron sa na farko da manema labarai bayan naɗa shi, Wike ya ce kafin ya amshi muƙamin minista sai da ya rubuta wasiƙar neman amincewa ga Shugaban Riƙo na PDP, Umar Damagum, Gwamnan Ribas wanda ya gaje shi, Siminalayi Fubara, Shugabannin Masara Rinjaye na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa, “kuma duk suka ce na je na karɓa.” Cewar Wike.
“Wa zai iya nuna mutum ɗaya ko ya faɗi sunan mutum ɗaya da na ke gaba da shi? Ku duba, su mutane sun fi so su riƙa yaɗa sharri da farfaganda. Wato ni dai na tsani mutanen da ba su faɗin gaskiya.
“Sun ce wai za su ladabtar da ni, wai don na karɓi muƙamin Minista.
“Shugaban Ƙasa ya rubuta wa gwamnoni 36 wasiƙa cewa kowanen su ya aika da sunayen waɗanda ya ke so a bai wa minista. Shin gwamnonin PDP ba su aika da sunayen waɗanda su ke so a naɗa ba? Ai kowane gwamnan PDP sai da ya rubuta wa Shugaban Ƙasa wasiƙa, tare da sunayen mutum 10 da ya ke so a cikin su za a ɗauki wanda ya ke so a naɗa minista.
“Amma ba su maganar kowa sai Wike. Har Shugaban PDP na Shiyyar Kudu maso Kudu da na Jihar Ribas sai da na aika masu da wasiƙar neman amincewar su. Kuma suka ce na karɓa kawai.
“Ina da shaidar amsoshin da aka aiko min. Saboda haka ku manta da ‘yan rawar kwambilo kawai. Kun san idan mutum ya rasa wata dama, shi ya jawo wa kan sa saboda girman kai, rawanin tsiya.” Cewar Wike.
Discussion about this post